Daga Rabiu Ali Indabawa,
Rahotanni daga Jihar Benuwe na nuni da cewa, ‘Yan sanda sun damke wata matashiya da ta banka wa saurayinta wuta sakamakon wani rikici da ya barke a tsaninta da shi a yankin Wadata da ke garin Makurdi.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, yarinyar mai shekaru 18 ta aikata wannan mummunan aiki ne a safiyar jiya da misalin karfe 2 na dare lokacin da saurayin nat ke tsaka da bacci mai nauyi.
A cewar majiyar, ihun da mutumin ya yi ne ya jawo hankalin makwabta da suka ruga don su taimaka masa amma kafin su kai ga hakan tuni ya ji rauni mai yawa na kunan wuta. “Nan da nan makwabta suka garzaya da shi zuwa ‘Makurdi Federal Medical Center, FMC,’ inda aka kwantar da shi,” in ji shi.
“Har yanzu ba mu san dalilin da ya sa ta aikata hakan ba. Har yanzu ba mu yi mata tambaya ba, amma zan iya tabbatar da cewa an kama ta kuma an kawo ta, a halin yanzu tana hannunmu. “Lamarin ya faru ne da misalin karfe 2:00 na safiyar jiya a titin Zaki Biam da ke Wadata. Za mu sanar da ku cikakken bayani, ”in ji PPRO.
Wannan sabon lamarin na zuwa makonni kadan bayan wani mutum mai shekaru 40, mai suna Nicodemus Nomwange, ya bankawa kansa da budurwarsa, Shiminenge Pam wuta a yankin High-Lebel da ke garin Makurdi. Bugu da kari kuma, a dai wannan lokacin, wata budurwa kuma ana zargin ta cinnawa masoyinta wuta a gidansa da ke titin Shaahu a cikin garin Gboko.