Tsohon ministan harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya taba zargin kasar Sin da cewa, tana hana ’yancin al’ummomin jihar Xinjiang na kananan kabilu bin al’adunsu. Dangane da wannan zargi, Aman Guli wadda take aiki a fannin al’adu dake gundumar Luopu ta jihar Xinjiang ta bayyana cewa, Mike Pompeo ba ya ji kunyar yin karya, kuma bai dace ya tsoma baki cikin harkokin jihar ba, domin bai taba zuwa wannan jiha ba. Tana mai cewa, mutanen jihar Xinjiang ne ke da ikon fadin yanayin zamansu.
Gundumar Luopu ta taba kasancewa gunduma mai fama da talauci, amma, cikin ’yan shekarun nan, ta kawar da talaucinta baki daya bisa taimakon gwamnati da kokarin da jami’ai da al’ummomi suka yi. A halin yanzu, an gina dakunan al’adu da dama a wannan gunduma, inda gwamnati da al’ummomi suka yi bukukuwan al’adu da dama.
Aman Guli ta ce, ita ’yar kalibar Uygur ce dake zaune a Jihar Xinjiang, ta san zaman rayuwar mutanen jihar, shi ya sa, ta ce, “ko Xinjiang na cikin kyakkywan yanayi ko akasin haka, mu mutanen jihar ne ke da ikon yanke hukunci, a maimakon wanda bai taba zuwa ba”. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)