• English
  • Business News
Wednesday, November 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yara 160,000 Ke Rayuwa Da Cutar Ƙanjamau A Nijeriya —NACA

by Idris Aliyu Daudawa
11 months ago
Yara

Shugabar hukumar hana yaduwar cutar kanjamo ta kasa (NACA) DoktaTemitope Ilori, ta ce har yanzu lamarin kokarin da ake  yi na hana da, ya dauki cutar daga wurin uwa, da kuma yara wadanda suke dauke da cutar har yanzu abin ya tsaya ne a kashi 33, wato bai kai ga kashi 95 da ake son cimmawa ba.

Da take jawabi da kuma tunawa da rahoton UNAIDS na shekarar 2023, Dokta Ilori ta ce ku san yara 160,000  da suke 0-14 suna rayuwa ne da cutar kan jamo a Nijeriya.

  • Tashin Farashin Kayan Masarufi Ya Fi Illa Ga Mazauna Jihohin Sakkwato, Edo Da Borno
  • Dalilan Da Suka Jefa ‘Yan Nijeriya Cikin Talauci Duk Da Karuwar Kudin Shiga – Masana

Shugabar ta bayyana hakan ne ranar Litinin a Abuja lokacin taron manema labarai kafin ranar cutar kanjamo ta shekarar 2024, mai taken: “A dauki hanyar da ta dace:  Ci gaba da amfani da maganin da ya dace, hana yaduwar cutar HIB tsakanin yara, saboda a kawo karshen cutar nan da shekarar ta 2030”.

Bikin ranar kanjamo ana yin shi ne kowace shekara 1 ga watan Disamba domin a samu wayar da kan al’umma dangane da cutar da kuma kwayar cutar da take sanadiyar ta.

A kan yadda cutar take har ila yau shugabar tace mutane milyan 1.4 ne masu shekaru daga 15 zuwa 64 da akwai mutane milyan biyu da suke rayuwa da cutar a Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu 

Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista

Bugu da kari kuma an samu mutane 22,000 da suka kamu da sabuwar cutar HIB sai kuma mutuwar mutane 15,000 a ko wace shekara.

“Nijeriya na da mutane da suka kai kashi 1.4 cikin 100, daga cikin al’ummarta masu shekaru daga,15 zuwa 64 da suka kai milyan 2 da suke rayuwa da cutar HIB.

“Kasar tana ci gaba da fuskantar matsala dangane da yadda ake kamuwa da cutar ko yadda ta ke shiga daga uwa zuwa danta tun yana cikin mahaifa. Rahoton UNAIDS na 2023 ya nuna kusan yara 160,000 da shekarunsu daga  0-14 ke rayuwa da cutar HIB, yayin da aka samu mutane 22,000 da suka kamu da cutar sai kuma  mutum 15,000 da suke mutuwa duk shekara,a  sanadiyar cutar kamar yadda ta yi bayani.

Sai dai kuma duk da hakan tace ma’aikatar lafiya ta tarayya da walwalar jama’a, kamar yadda Dokta Ilori ta bayyana  bada dadewa bane ta kafa wani kwamitin kasa wanda zai domin ya tabbatar da ana aiwatar da abinda aka yi niyyar yi.

Ta kara jaddada NACA ta kaddamar da kwamiti a Jihohi uku inda ta fara magana kai tsaye da gwamnoni uku su bada taimako  kaddamarwar da za’ayi, da kuma samar da wani kwamiti kamar  shi  a zaman na bangaren Jiha,da niyyar tabbatar da ba wani jaririn da za’a sake haifa dauke da cutar HIB  a Nijeriya.

“Wannan abin haka zai kasance a Jihohi 36 da babban birnin tarayya bada dadewa ba ,”  ta kara jaddada shirin hukumar dake yi ma jagoranci da zata ci gaba duk wasu tsare- tsaren taimakawa kawo karshen cutar kanjamo, koda kuwa ace su masu taimakawar za su nuna gazawa ko su bari.

“Tawaga ta, ta dade tana ganawa da masu ruwa da tsaki kan lamarin HIB wajen taimakawar da suke yi, inda har ma suna samar da wani hali na yiyuwar ci gaba dayin hakan domin kada a bari a tafka asarar nasarar da aka fara samu.Daga nan kum a samu damar sa gwamnatcin Jihohi a cikin lamarin inda ita ma za ta bada nata taimakon wajen samar da duk abubuwan da ake bukata lokacin aiwatar da tsarin a Jihohi.

“Manufar wannan dabarar kamar yadda ta yi karin bayani koda ace su masu taimakawa sun daina, babu wani abinda zai tada hankalin kasa, idan dai ana maganar matakan hana yaduwa da kawo karshen cutar HIB, har ma da wasu cututtukan da suke da alaka da ita.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Majalisar Kano Na Shirin Zartar Da Dokar Gwajin Kwayoyin Jini, Kanjamau Da Cutar Hanta Kafin Aure
Manyan Labarai

Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu 

November 5, 2025
Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista
Labarai

Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista

November 5, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio
Labarai

Majalisar Dattawa Ta Amince da Naira Tiriliyan 1.1 Don Biyan Bashin ‘Yan Kwangila – Akpabio

November 5, 2025
Next Post
Yunkurin ACF Na Mara Wa Dan Takarar Arewa Baya A 2027 : Ta Ina Za A Fara?

Yunkurin ACF Na Mara Wa Dan Takarar Arewa Baya A 2027 : Ta Ina Za A Fara?

LABARAI MASU NASABA

Majalisar Kano Na Shirin Zartar Da Dokar Gwajin Kwayoyin Jini, Kanjamau Da Cutar Hanta Kafin Aure

Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu 

November 5, 2025
Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka

Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka

November 5, 2025
Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista

Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista

November 5, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

Majalisar Dattawa Ta Amince da Naira Tiriliyan 1.1 Don Biyan Bashin ‘Yan Kwangila – Akpabio

November 5, 2025
An Nemi Kasashen ECOWAS Su Samar Da Kariya Ga Yankunan Hakar Ma’adanai

ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya

November 5, 2025
Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86

Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86

November 5, 2025
Ɗan Majalisar Amurka Ya Zargi Kwankwaso Da Hannu A Kisan Kiristoci A Nijeriya

Ɗan Majalisar Amurka Ya Zargi Kwankwaso Da Hannu A Kisan Kiristoci A Nijeriya

November 5, 2025
Sanata Barau Ya Tsaya Takarar Shugaban Majalisar Dattawa

Ba Na Jin Tsoron Trump – Martanin Sanata Barau Ga Akpabio

November 5, 2025
CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika

CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika

November 5, 2025
Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma

Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma

November 4, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.