Asusun kula da ilimin yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ce, a kalla yara miliyan daya ke mutuwa a kowace shekara a Nijeriya a cikin watansu na farko da haihuwa, lamarin da ke nuni da cewa kaso 10 cikin 100 a duniyance.
Jami’in lafiya na ofishin UNICEF da ke Bauchi, Oluseyi Olosunde, shi ne ya shaida hakan a wani taron kara wa juna sani na wuni guda da aka shirya wa ‘yan jarida kan yawan mace-macen yara a Bauchi, Gombe, Taraba da ya gudana a Jos ta jihar Filato.
- Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Ƙaddamar Da Biyan Bashin Waɗanda Aka Tsare A Gidan Gyaran Hali
- Batun Tuhumar Ƙananan Yara Da Laifin Shirya Juyin Mulki
Ya ce bisa adadin mace-macen da ke faruwa a Nijeriya, ya nuna cewa, yara miliyan 1 ke mutuwa a farkon watansu na farko a duniya.
Jami’in ya ce a kowace rana, Nijeriya ta rasa yara ‘yan kasa da shekaru biyar su 2,300, inda ya ce, mafi yawan wadannan mace-macen suna wakana ne a yankunan karkara, inda kuma a kalla yara 157 ke mutuwa a yankunan karkara kullum.
Ya kara da cewa bisa abubuwan da suke janyo mutuwar yaran sun hada da talauci da karancin asibitocin kula da yara, wanda ke janyo rashin samun kulawar kiwon lafiya.
Ya ce, sauran hanyoyin da suke janyo mutuwar sun hada da haihuwa bisa kan al’adar da aka saba, rashin ilimi, karancin abinci mai gina jiki da karancin wayarwa.
A nata jawabin, Dakta Ruth Adah, wata kwararriya a asibitin koyarwa na jami’ar Jos, ta lura kan cewa akwai bukatar a tashi tsaye wajen amfani da dokokin kariya ga rayuwar yara domin rage yawaitar mace-macensu da ake fuskanta.
Ta ce, duk da Nijeriya ana yawan samun mace-macen yara, amma Jihar Bauchi, Gombe da Taraba su ne kan gaba wajen samun mace-macen yara kanana a fadin Nijeriya.
Adah ta jinjina wa UNICEF bisa shirya taron bita wa ‘yan jaridan, tana mai cewa wannan ya zo a kan gaba domin samun dama da hanyoyin wayar wa jama’a da gwamnatoci kai, kan yadda a dauki matakan da suka dace wajen rage yawaitar mace-macen yara a cikin al’umma.