Ana ‘yan makonni zuwa babban zaben 2023, fagen siyasar kasar nan yana kara zafafa inda manyan jam’iyyun biyu na ci gaba da yi wa juna yarfe, kazafi da sharin aikata cin-hanci da almundahana a tsakaninsu.
Bangaren dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar suke jifar juna da wadannan zarge-zargen.
- Naja’atu: Cikon Banci Ce A Wurinmu, Tun Da Muka Kore Ta Take Ta Sambatu – APC
- Karin Bayani Kan Harin Bom Din Da Ya Kashe Fulani 39 A Nasarawa — Ganau
Jam’iyyar APC ce ta fara harbo mizal din. Kusan mako daya daya wuce ne kwamitin yakin neman zaben Tinubu/Shettima ya nemi a gaggauta kamawa tare da hukunta dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar saboda zargin badakalar kudade da suke zargin ya aikata tare kuma da aikata manyan laifuka.
Kungiyar ta bayyana haka ne a taron manema labarai da ta kira a Abuja inda ta kara da cewa, Atiku bashi da wani kariya na tsarin mulki da zai hana a kama shi tare da hukunta shi, shugabanin bangaren watsa labarai a kwamitin yakin neman zaben Tinubu da suka hada da Dele Alake, Festus Keyamo, Bayo Onanuga, Femi Fani-Kayode, da kuma Idris Mohammed suka jagoranci taron manema labaran, sun kuma nemi Atiku ya gaggauta yin murabus daga takarar shugabancin kasa da yake yi tare da ba wa al’ummar Nijeriya hakuri a kan zargin da ake yi masa na karkatar da kudaden al’umma zuwa aljihunsa.
Sun kuma yi alkawarin garzayawa kotu don dakatar da takarar da yunkurin da tsohon mataimakin shugaban kasar yake yi na zama shugaban kasa a zaben da za a gudanar wata mai zuwa. Wannan zargin yana zuwa ne bayan da wani tsohon hadimin Atiku, Mista Michael Achimugu, ya yi zargin cewa, Atiku ya yi amfani da shirin nan na sayen motocin SPB wajen kwasar kudade daga tsohon Gwamnan Jihar Filato Joshua Dariye wanda kotu ta daure saboda badakalar kudaden kare zaizayar kasa na Jihar Filato. Tuni dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi masa afuwa. A lokacin da Atiku yake mataimakin shugaban Nijeriya daga 1999 zuwa 2007, Dariye na a matsayin gwamna ne a daidai lokacin.
A ranar Lahadi 22 ga watan Janairu 2023, bangaren kwamitin yakin neman zaben Atiku suka mayar da nasu martanin, inda suka bukaci hukumar yaki da fataucin miyagin kwayoyi NDLEA da hukumar EFCC su gaggauta kama dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Bayanin haka yana kunshe ne a jawabin da mambobin kwamitijn yakin neman zaben jam’iyyar PDP suka yi a ta bakin Bashorun Dele Momodu, Daniel Bwala, Mista Paul Ibe da kuma mataimaki na musamman ga Atiku a kan harkar yada labarai, Phrank Shaibu a ganawar da suka yi manema labarai.
A cikin jawabin su, Shaibu ya lura da cewa, Nijeriya na fuskantar wai yanayi da ya kamata a yi takatsanstan wajen zaban wanda zai zama shugaban kasa nag aba , kuma duk wani kuskure da za a yi zai iya zama bala’i ga kasa baki daya. Ya kara da cewa,“Nijeriya na fuskantar matsalolin da suka hada da na ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran miyagun ayyukan ta’addanci wadanda kuma suke da alaka da tu’ammali da miyagun kwayoyi. “A saboda haka zai iya zama tashin hankali in aka zabi wanda rayuwarsa ke tattare da badakalar harkar kwaya da safarar ta.”
Ya bayyana cewa, Tinubu na fuskantar badakalar Dala 460,000 wanda ake zargin ya samu ne daga badakalar safarar miyagun kwayoyi a kasar Amurka, ya kuma kamata a kara zurfafa bincike don gano cikakiyyar gaskiyar lamarin. “A kan haka muna kira ga hukumar NDLEA su gagaggauta kama Bola Ahmed Tinubu su kuma tabbatar da hukunta shi.
Wananan takaddamar da yarfe a tsakanin manyan jam’iyyun kasar nan abu ne da zai iya tayar da kura a sararin samaniyar harkokin siyasar kasar nan kamar yadda kungiyar Afenifere ta ankarar ta bakin sakatarenta na kasa Kwamrade Jare Ajayi, amma kuma wannan yana kara fitowa ne da lamarin cin-hanci da rashawa matsayin wani abin da yakamata ya zama a kan gaba a cikin abubuwan da yakamata a rika tattauanwa a fagen yakin neman zabe a tsakanin jam’iyyun kasar nan.
Abin lura a nan shi e dukkan jam’iyyun kasar masu neman shugabancin kasar na ikiirarin za su jagoranci yaki da cin-hanci da rashawa in kai ga ci.
Za a iya fahimtar yadda matsalar cin-hanci da rashawa ta yi katutu a harkar kasar nan in aka lura da cewa, kungiyar ‘Transparency International (TI)’ ta ayyana Nijeriya a matsayin kasar da ke a kan gaba a cikin kassashen da aka fi cin-hanci da rashawa a duniya, saboda haka tabbas ya kamata lamarin cin-hanci da rashawa ya zama a kan gaba kuma ma’auni na alkawurran da manya jam’iyyumu za su yi amfani da su wajen yakin neman zaben da ake yi a halin yunzu a shirye-shiryen fuskantar zaben 2023.
Yana da matukar muhimmanci hukumomin da abin ya shafa su tabbatar da bincikar zarge-zarge biyu da bangarorin suka yi wa junansu. Bai kamata a yi watsi da zarge-zargen ba.
Ganin iri wannan zarge-zarge masu tayar da hankali ne a kan manyan ‘yan takarar shugabancin kasar a halin yanzu al’amura duk sun koma a hannun ‘yan Nijeriya masu dauke da katin zabe, ya kamata su yi karatun ta natsu su zabawa kasar nan wanda ya fi dama-dama don daga dukkan alamu tsakanin manyan ‘yan takarar shugabancin kasar nan duk gautar ja ce.