A yau Litinin ake saka ran za a ƙarkare tattaunawa kan mafi ƙarancin albashi tsakanin Gwamnatin Nijeriya da Ƙungiyar Ƙwadago ta NLC/TUC bayan dawowar ƙungiyar daga halartar wani taro a ƙasar Geneva.
Ƙungiyar Ƙwadagon dai ta rage farashin abunda ta ke buƙata daga ₦494,000 zuwa ₦250,000 inda ita ma gwamnatin Nijeriya a nata bangaren ta yi alƙawarin ƙara ₦2,000 daga tayin ₦60,000 zuwa ₦62,000.
- Da Dumi-Dumi: NLC Da TUC Sun Janye Yajin Aiki
- Yajin Aiki: Ƙungiyar Ƙwadago Ta Rufe Filayen Jirgin Saman Legas Da Abuja
Kawo dai yanzu kallo ya koma kan gwamnatin Nijeriya da Ƙungiyar Ƙwadago don ganin ko za su iya samun daidaiton da ya dace da bukatun juna, la’akari da ƙalubalen tattalin arzikin da ƙasa ke fuskanta.
A makon da ya gabata Kungiyar Kwadago ta shiga yajin aikin gama-gari a fadin kasar kafin daga bisani kungiyar ta janye bayan kiraye-kirayen komawa teburin sulhu da tsagin gwamnati don samun daidaito.