… ci gaba daga makon da ya gabata.
Tarihin Yajin Aikin ASUU.
A shekarar 1980, a lokacin mulkin soja, ƙungiyar ta shiga cikin ƙungiyoyin da ke adawa da gwamnatin soja. Tarihi ya nuna cewa, sakamakon haka, ƙungiyar ta shirya yajin aikinta na farko a shekarar 1988 don neman samun ‘yancin kai ga jami’o’i da albashi mai kyau.
Tasirin tsarin Bankin Duniya (WB) da Asusun Kuɗi na Duniya (IMF) da aka ƙaƙaba wa Nijeriya wanda ya aiwatar da tsarin daidaito na ‘yancin cinikayya na (SAP) shi ya fara sanya ASUU tsunduma yajin aiki. Tsarin ya jefa ma’aikatan ilimi cikin mawuyacin hali saboda rashin aiwatar da Tsarin Albashi na Jami’a.
Sakamakon haka, gwamnatin soji a wancan lolaci ta ayyana ASUU a matsayin haramtacciyar ƙungiya a ranar 7 ga Agusta, 1988, kuma aka ƙwace dukkan kadarorinta.
Amma bayan wannan yajin aikin, an sake bata lasisinta na ci gaba da zama halastacciyar ƙungiya a shekarar 1990, kuma a ranar 23 ga Agusta, 1992, aka sake haramta ta. A ranar 3 ga Satumba, 1992, aka yi wani zama wanda ya tanadar wa ķungiyar wasu yarjejeniyoyi da ta amince da wasu manufofin ƙungiyar, ciki har da haƙƙin ma’aikata na shiga cikin yarjejeniyar gama gari.
A shekarun 1994 da 1996, ASUU ta gudanar da wani yajin aiki don nuna rashin amincewa da gwamnatin soja kan korar ma’aikata da Janar Sani Abacha ya yi.
A ranar 17 ga Disamba, 2013, ASUU ta ayyana yajin aikin da ya ɗauki tsawon watanni shida kan rashin aiwatar da yarjejeniyar 2009 tsakaninta da gwamnatin tarayya, wanda daga ƙarshe aka dakatar da yajin aikin bayan da ƙungiyar ta amince da wasu yarjejeniyoyi. Duk da haka, shekara guda bayan haka, ƙungiyar ta ci gaba da yajin aikin gargaɗi na mako guda kan gazawar gwamnati wajen aiwatar da yarjejeniyar 2009 da kuma yarjejeniyar 2013.
A cewar ƙungiyar: “Ba a aiwatar da ɓangarori da yawa na yarjejeniyar 2013 da yarjejeniyar 2009 da gwamnatin tarayya ta yi alƙawari ba”. Yarjejeniyar ta haɗa da biyan haƙƙoƙin mambobinta da aka riƙe tun daga Disambar 2015, kuɗaɗen farfaɗo da jami’o’i, tsarin fansho, tsarin tara kudi a asusu ɗaya (TSA) da ‘yancin kai na jami’o’i da sake tattaunawa batun yarjejeniyar 2009 sannan kuma, tsarin manufar gwamnati ta “babu aiki, babu albashi” dole a dakatar da ita.
Yajin Aikin ASUU daga 1999 – 2022
Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta fuskanci yajin aiki da dama tun daga shekarar 1999, inda aka fi yin yajin aiki a shekarar 2003, 2010, 2013, 2020, da 2022, galibi saboda rashin aiwatar da yarjejeniyoyi da gwamnati ke yi wurin fitar da kuɗaɗen jami’o’i. Yajin aikin da ya fi tsayi ya faru ne a shekarar 2020 (watanni 9) da kuma 2022 (watanni 8).
A cewar ASUU, waɗannan yajin aikin, an gudanar da su ne don tilasta wa ɓangaren gwamnati aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma. Don haka, ƙungiyar ta ASUU tana ƙoƙarin matsa wa gwamnati lamba don ɗaukar matakan da suka dace, amma wannan yana yin illa ga ɗaliban jami’o’i.
Ga jerin yajin aikin da ƙungiyar ASUU ta gudanar tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya:
1999 – Watanni 5
2001 – Watanni 3
2002 – Makonni 2
2003 – Watanni 6
2005 – Makonni 2
2006 – Kwanaki 3
2007 – Watanni 3
2008 – Mako 1
2009 – Watanni 4
2010 – Watanni 5
2011 – Kwanaki 59
2013 – Watanni 5
2017 – Watanni 1
2018 – Watanni 3
2020 – Watanni 9














