Daga Maje El-Hajeej Hotoro
‘Yan Kwankwasiyya Da ‘Yan Gandujiyya Sun Cika Kotu yayin da Dan majalisar dokokin Jihar Kano da ke wakiltar karamar hukumar Birni Baffa Babba Dan Agundi ya bayyana a gaban kotun majistire ta Jihar Kano domin neman ba’asin bata suna da ya ke zargin Abdullahi Tanka Galadanci da aka fi sani da (BOKAN SIYASA) ya yi masa gami gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
A cewar mai gabatar da kara Barista Sunday O. Ekwe ya bayyana wa kotu cewa, a wani shirin siyasa da ake gabatarwa a wani gidan Rediyo mai zaman kansa (Rahma Rediyo FM) Tanka Galadanci ya zargi Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da zargin ba wa ‘yan majalisar dokokin jihar cin hancin mota kirar CRB. A cewar Dan Agundi, motocin an sayo kowacce akan Naira Miliyan 16.5 amma Tanka ya yi ikirarin ba su wuce Naira Miliyan 8 ba. Kana kuma Samfurin 2013 ne maimakon 2016 da gwamnati ta ayyana. Bugu da kari ‘yan majalisar sun karbi cin hanci daga wajen dan kwangilar ne domin shirya wannan kitumurmura.
Wannan furuci ya cutar da ‘yan majalisar dokokin Jihar Kano, sakamakon munana musu zato da magoya bayan su ke yi. Sai dai lauyan Tanka da ake zargi Barista Usman Umar Fari ya roki kotu da ta daga karar domin hada wasu bayanai. Kana kuma mai shari’a Muktari Dandago ya daga zaman zuwa 12 ga watan Oktoba 2017.
A baya ‘yan sanda sun gurfanar da Bokan siyasa sau 15 da zargin bata suna. A yayin zaman kotun ‘yan Kwankwasiyya da ‘yan Gandujiyya sun cika kotun domin nuna halacci ga bangarorin da kowa ke goyon baya.