Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
A shekaran jiya Alhamis ne dai Majalisar Dinkin Duniya ta ware na musamman domin zaman lafiya ‘International Peace Day’, inda aka gabatar da taron a wasu sassan duniya cikinsu har da Nijeriya.
A jihar Bauchi ma gamayyar kungiyoyin zaman lafiya sun yi gangamin wayar wa jama’a kai dangane da muhimmancin zaman lafiya hade da bukatar al’umma a kowane bangare da su kasance masu mutunta zaman lafiya domin matukar muhimmancin da hakan ke da shi a tsakanin al’umman Nijeriya.
Shugaban kungiyar gamayyar kungiyoyin Mista Samuel Yelmism ya ce zaman lafiya abu ne mai makutar muhimmanci a tsakanin al’umman duniya, jiha da kasar nan baki daya.
Shugaban wanda ya samu wakilcin Mista Ayuba Mainas ya ce, Majalisar Dinkin Duniya ce ta ware rana domin yayata muradin zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’umman duniya, kasancewar yadda zaman lafiya ke da matukar muhimmaci a tsakanin al’umma.
Ya bayyana damuwarsa kan abubuwan da suke faruwa a wadansu sassan kasar nan ta Nijeriya na tashin-tashina da fitina da wasu ke jawowa bisa son zuiyarsu. Sai ya yi kira ga hukumomin da abun ya shafa da su magance matsalolin da suke addabar Nijeriya, na tashin-tashina da wasu tsaruru ke haifar wa kasar, a bisa son ransu na kashin kai.
A cewarsa gamayyar kungiyar, wacce suka fito a karkashin kungiyar DEC za su ci gaba da bada goyon baya ga dukkanin shirye-shirye da za su kawo zaman lafiya da kyautata rayuwar marasa galihu a jihar nan da ma kasa baki daya.
Mista Samuel wanda ya bayyana cewar sakamakon tashin hankula da rikicin da suka faru da daman mutane sun zama marayu da marasa galihu. Sai ya bukaci kafafen yada labarai da su bada tasu gudunmawar wajen tabbata da zaman lafiya da ci gaban kasar nan ta Nijeriya, ta hanyoyin da suka dace da aikin nasu, musamman wajen fadakar da jama’a kan muhimmancin zaman lafiya da mutunta juna.