Daga Balarabe Abdullahi, Zariya.
Tsohon Kakakin Majalisar Jihar Kaduna, Alhaj Ahmed Hassan Jumare (BRANCO), ya shawarci gwamnatin tarayya da ta tabbatar ta yi hukunci mai tsanani ga waɗ anda suke neman durƙusar da ƙasar nan, ɓangaren da ya shafi haɗ in kai a tsakanin ‘yan Nijeriya.
Alhaji Ahmed Hassan Jumare ya bayyana haka ne a tsokacin da ya yi na cikar Nijeriya shekara 57 da samun ‘yanci daga turawan mulkin mallaka, a shekara ta 1960.
Ya ci gaba da cewar dole al’ummar Nijeriya su gode wa shugabannin da suka gabata,na yadda suka yi bakin ƙoƙarinsu na ganin sun ciyar da Nijeriya da kuma ‘yan Nijeriya gaba a fannoni da dama,kamar aikin gona ilimi da tattalin arziki da kiwon lafiya da dai sauran fannoni masu yawan gaske.
Wannan mataki ko kuma matakai da gwamnatin tarayya za ta ɗ auka,a cewar Alhaji Ahmed Hassan Jumare,ya zama gani-ga-wane da ake cewa ya isa wane tsoron Allah.Daga nan sai a sami mafita daga masu son tayar da fitina da cewar shi ne hanyar da suke rayuwa.
A kuma tsokacin da ya yi kan ci gaban da aka samu a Nijeriya daga shekara ta 1960 zuwa wannan shekara ta 2017, Alhaji Ahmed Hassan Jumare ya ce babu shakka an sami ci gaba a ɓangarori da dama,kamar ilimi,da lokacin da aka sami ‘yancin kai, ba kowa ne gari ko ƙauye ne ke da makarantu ba, haka ya ke a ɓangarorin kiwon lafiya da hanyoyi da tattalin arziki da kuma sauran ɓagarori da dama.
Wannan ma kawai a ceawrsa ya da ce ‘yan Nijeriya da su tashi tsayena ganin sun yi abubuwanda za su ciyar da ƙasar nan gaba ta ko wane fanni da za su iya,ba su riƙa neman mayar da hannun agogo bay aba ga halin da Nijeriya ke ciki na batun zaman lafiya da kuma ɗ unkewarta a shekaru masu zuwa.
Da kuma ya juya ga shugabanni,musamman a cewarsa masu jagorancin Nijeriya a yau,da ya dace da su riƙa sauraron shawarwarin al’ummar da suke yi wa jagoranci.Ya ƙara da cewar,ka da shugaba ya ɗ auka in an ba shi shawara, a na so ya gyara tafiyar mulkinsa ne, ba sukansa a ke yi ba.
Alhaji Ahmed Hassan Jumare Branco ya tabbatar da cewar,alamu sun nuna jama’ar Nijeriya sun fahimci bambancin jiya da yau, kuma ya ce fahimtar haka alamu ne da suka nuna za a yi karatun baya, domin gane karatun da za a yi a gobe.