Daga Sabo Ahmad
Kwamitin da Shugaban Ƙasa ya kafa kan kula da ‘yan gudun hijira na Arewa-maso-gabas, ya bayyana damuwarsa bisa ƙaruwar da ake samu na yawan fyaɗe da barazanar da ‘yan gudun hijirar ke fuskanta na rayukansu da dukiyoyinsu a sansanoninsu da ke Arewa-maso-gabas.
Kwamitin ya bayar da ƙiyasin cewa, kimanin yara 30 ne aka yi wa fyaɗe a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke jihar Yobe, a cikin watan Satumba na shekara ta 2017.
Kwamitin ya ƙara da cewa, barazanar fyaɗen ga yara da manyan mata ta ƙara ƙazanta a wannan watan da muke ciki, wanda kuma ya sa ake fargabar ƙara yaɗuwar ƙwayoyin cutar ƙanjamau a sansanonin. Mataimakin shugaban kwamitin, Alhaji Tijani Tumsa, ne ya bayyana haka lokacin da suke tattauna wa da wakilan kwamitin, ranar Alhamis ɗin da ta gabata a Abuja, wanda kuma ya nuna damuwar da Majalisar Tarayya ta yi kan wannan mummunan aiki.
Tumsa ya dangata faruwar wannan al’amari da rashin cikakken tsaron da ake fama da shi a sansanonin ‘yan gudun hijirar, saboda haka, ya ce, kwamitinsu zai haɗa kai da jami’an tsaro, wajen ganin an kawo ƙarshen wannan matsala.
“Fyaɗe mummuna abu ne, musamman da yake hanya ce ma fi sauƙi ta yaɗa ƙwayoyin cutar ƙanjamau; saboda haka, abin da muka sa a gaba shi ne, duk wanda aka kama shi da wannan laifi za a yi masa hukuncin da ya dace, cikin gaggawa.” In ji shi.
Da ake tambayarsa kan yawan mutanen da suka kama bisa zarginsu da aikata wannan mummunan hali sai ya ce, ba shi da masaniya a kan yawan mutanen da aka kama, amma dai ya tabbatar da cewa, dukkan waɗanda aka Kaman suna tsare.
Ya ce, Kwamitin nasu na ƙoƙarin koya wa ‘yan gudun hijirar sana’o’i, yadda ko bayan sun koma gida za su ci gaba da gudanar da rayuwarsu cikin walwala.