Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home LABARAI

Yin Rangwame A Harkar Kasuwanci ke Jawo Albarka   -Shehu Dan Kwarai

by Muhammad
March 20, 2021
in LABARAI
2 min read
Kasuwanci
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Ibrahim Muhammad,

A ci gaba da irin gudumuwar da wasu ‘yan kasuwa ke bayarwa na daukar matakai na bunkasa harkar kasuwancinsu da kuma sama wa matasa aikin yi, an sake bude wani karin shagon zamani na saida kayayyaki na ‘Shehu Dan Kwarai Inbestment’ a Kasuwar Kantin Kwari da ke Kano, inda aka bayyana cewa yin rangwamne a kasuwanciu yana jawo albarka ga arziki.

Taron bude wannan katafaren shagon ya sami halartar ‘yan kasuwa da dama da suka taya murna da wannan ci gaba da aka samu na zamanantar da harkar kasuwanci.

Da yake zantawa da manema labarai a yayin taron, Shugaban rukunin Kantunan ‘Shehu Dan Kwarai, Alhaji Shehu Abdulkadir Badamasi da janar Manajansa, Alhaji Abdulrahman Abdulkadir da aka fi sani da ‘Family’ ya yi bayani a madadinsa, ya bayyana cewa a kalla yanzu akwai ma’aikata da suke aiki a kantunan a Kano da ake biya kullum su guda 300, wannan wani kokari ne na tallafa wa matasa da sana’o’i.

Ya ce, sannan akwai wasu da suke a jihohin Legas da Fatakwal da kuma wasu kasashe daban-daban da suke huldar kasuwanci da su.

Yana mai cewa yanzu haka Shehu Dan Kwarai Inbestment’ na da manyan shaguna na zamani guda uku da kuma shaguna na kasuwa guda bakwai da a kullum ake hada-hada da jama’a da ke ciki a wajen kasar nan.

Ya ce suna mu’amala ne da dubban abokan hulda a kullum, wanda suka hada da masu zuwa su sari kaya su kai rumfunansu a kasuwar Kantin Kwari su sayar saboda rangwame da suke samu.

Ya kara da cewa akwai abokan hulda da suke mu’amala da su ta saye da sayarwar a internet ‘online,’ wanda idan suka kawo kaya Kwantena sai ka taras tuni an sayar ta ‘online’ kafin ma a bude, shi ya sa  wani lokacin sai wanda ake tare da su a kasuwar da suke sara in suka ga kaya aka ce musu an riga an sayar, sai wasu su dauka an ki sayar musu ne.

Janar Manajan na ‘Shehu Dan Kwarai inbestment,’ Alhaji Abdurrahman Abdulkadir ya ci gaba da cewa, wannan sauki da suke da shi a hakar kasuwancin ya sa har wasu ‘yan kasuwa ke musu zargin cewa suna bata kasuwa, ita kuwa kasuwa abin da yake sanya mata albarka, shi ne rangwame. Don haka ya kamata ‘yan kasuwa su rika sa tausayi da hakuri da karamar riba mai albarka.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Rayuwar Dauda Dangalan Ta Sadaukarwa Ce Ga Al’umma  -Ja’afar Sani

Next Post

Dalilin Da Ya Sa Na Kagi Yin Garkuwa Da Kaina  In Ji Amaryar Kano

RelatedPosts

Kogi

‘Yan Bindiga Sun Sace Ma’aikatan Jinya Biyu A Kaduna, Matafiya 18 A Oyo

by Muhammad
23 mins ago
0

Kwanaki biyu da sace daliban jami'ar Greenfield da ke jihar...

Sace Daliban Jami’a A Kaduna: Yadda ‘Yan Bindiga Suka Shammaci Jami’an Tsaro

Sace Daliban Jami’a A Kaduna: Yadda ‘Yan Bindiga Suka Shammaci Jami’an Tsaro

by Sulaiman Ibrahim
5 hours ago
0

Daga Abubakar Abba, Kaduna A daren ranar Talata da dare...

Gwamnan Gombe Ya Nuna Takaicinsa Kan Masu Gina Gidajen Mai A Unguwanni

Gwamnan Gombe Ya Nuna Takaicinsa Kan Masu Gina Gidajen Mai A Unguwanni

by Sulaiman Ibrahim
5 hours ago
0

Daga Khalid Idris Doya, Gombe Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu...

Next Post
Amarya

Dalilin Da Ya Sa Na Kagi Yin Garkuwa Da Kaina  In Ji Amaryar Kano

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version