Zaɓen 2019: PDP Ta Gargaɗi ‘Ya’yanta Su Kiyaye Dokar INEC

Daga El-Mansur Abubakar, Gombe

Ƙungiyar ci gaban Haruna Garba dake kiran Ambasada Haruna Garba Magayaƙin Gombe da ya amsa kiransu ya fito takarar kujerar gwamnan jihar Gombe a zaɓen shekarar  2019 ta Haruna Garba Solidarity group a karkashin tutar jam’iyyar PDP ta gargaɗi mambobinta da su kiyaye dokokin INEC.

Wannan gargaɗi da ƙungiyar tayi yana dauke ne a wata takarda da suka aikewa yan jarida ranar Laraba a Gombe mai dauke da sanya hannun Alhaji Yari Na Alhaji Gambo Isari.

Da suke yabawa hukumar zaɓen ta kasa INEC kan jadawali da lokutan zaɓe da hukumar ta fitar na zaɓen shekara ta 2019 sun lura hukumar zaɓen ta Ja kunnen jam’iyyun siyasa da yan takara na kaucewa fara gudanar a tarukan siyasa da yaƙin neman zaɓe tunda lokaci bai yi ba.

Har Ila ƙungiyar ta Haruna Garba solidarity group ta sake gargaɗin mambobinta da magoya bayan Sanata Haruna Garba da su gujewa ayyukan da suka saɓawa tsarin dokokin hukumar zaɓen ta INEC dan gudun samun matsala.

Ƙungiyar ta yi amfani da wannan damar ta shaidawa duniya cewa su masu biyayya ne ga tsarin doka sannan kuma za su kiyaye gudanar da ayyukan da suka saɓawa dokar kasa da ta hukumar zaɓen ta INEC.

“ Babu wani ko wata da yake ikirarin nuna goyon bayansa ga Sanata Haruna Garba da zai yi amfani da sunan wannan ƙungiyar ya karya dokar hukumar zaɓe ta INEC “ A cewar ƙungiyar.

Daga nan sai Alhaji Yaro Na Alhaji Gombo Isari, a ƙungiyance yace suna nemi hadin kan yan jarida a fadin jihar Gombe wajen taimakawa suna yayata aikace- aikacen ƙungiyar dan a san abubuwan da suke gudanarwa.

Idan dai za’a iya tunawa hukumar zaɓen ta INEC a kwanakin baya ne  ta fitar da tsarin jadawali da ranakun zaɓuɓɓukan dake tafe na shekarar ta 2019 inda za’a gudanar da zaɓen shugaban kasa dana yan majalisun Tarayya a ranar 16 ga watan Fabarairu.

Zaɓen gwamnoni da yan majalisun jihohi zai gudana a ranar 2 ga watan Maris kuma dukkan yaƙin neman zaɓe an hana har sai saura kwanakin 90 Kafin ranar zaɓe.

 

Exit mobile version