Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana alhininsa game da rasuwar Alhaji Aminu Dantata, inda ya bayyana shi a matsayin babban attajiri kuma mai kyautatawa.
Buhari ya ce Dantata ya bada gagarumar gudummawa a harkar taimakon jama’a da kuma kasuwanci, inda hakan ya taimaka wajen sauya rayuwar mutane a Nijeriya da ma wajen ƙasar.
- Hukumar NPA Na Son Tara Kuɗaɗen Shiga Naira Tiriliyan 1.2 A 2025
- Har Yanzu Ba Mu San Inda Za A Binne Dantata Ba — Sakatarensa
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce marigayi Dantata ya tallafa wa ilimin addinin Musulunci, kiwon lafiya, harkar kasuwanci da kuma ci gaban yankunan karkara.
“Dantata ba kawai attajiri ba ne,” in ji Buhari, “Mutum ne da ya horar da matasa masu sha’awar kasuwanci. Yanzu su ma suna taimaka wa wasu kuma suna kyautatawa kamar yadda ya koya musu.”
Buhari ya ƙara da cewa miliyoyin mutane a faɗin Yammacin Afirka sun amfana da taimakon Dantata.
Ya ce yana matuƙar daraja lokutan da suka gudanar tare.
Ya roƙi Allah ya bai wa iyalan Dantata da Dangote, Masarautar Kano, da al’ummar jihar da ƙasar baki ɗaya haƙuri da juriyar rashin wannan babban mutum.
“Allah Ya jikan shi Ya sa Aljannatul Firdaus makomarsa,” in ji Buhari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp