Abubakar Abba" />

Za A Fara Gangamin Allurar Foliyo A Kaduna

Shugaban kungiyar ‘yan jarida masu yaki da ciwon foliyo reshen jihar Kaduna (JAP) Alhaji Lawal A. Dogara ya sanar da cewar, za a fara gangamin allurar foliyo ta watan Afirilun shekarar 2018.

A cikin sanarwar da Shugaban ya sanya wa hannu ya kuma bai wa jaridar LEADERSHIP a Kaduna,ta ce, za a fara gudanar da gangamin ne daga ranar biyar zuwa ranar goma na watan Afirilun shekarar 2018.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, za a gudanar da gangamin ne a kan titunanan da gida-gida da kasuwanni da tashoshin mota da kuma manyan tituna da sauran su.

Saboda haka, sai kungiyar ta yi kira ga iyaye da masu kula da yara da su tabbatar da sun mika ‘yayan su don a yi masu allurar a lokacin gudanar da gangamin da kuma ci gaba da allurar  da aka saba yi a cibiyoyin da asibitocin da ke kusa da su.

Kungiyar ta yi kira da tattausar murya ga sarakuna da malaman addinai da ka da su gajiya a kan goyon bayan da suka saba bada wa don cin nasarar yakar ciwon na foliyo a dukkan fadin jihar.

A cewar kungiyar ta JAP, gwamnatin jihar da Hukumar kiwon lafiya matakin farko ta jihar (SPHCDA) da masu bayar da tallafi da kuma masu ruwa da tsaki, sun  kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace don gudanar da aikin a cikin nasarar aikin.

 

Exit mobile version