Gwamnatin Tarayya ta ce aikin titin jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Kano zai kammalu a shekarar 2026.
Ministan sufuri, Sa’idu Ahmed Alkali, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba.
- Sin Ta Dade Tana Aiki Tukuru Kan Kiyaye Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali Na Yanki
- Ma’aikatar Bunƙasa Harkar Kiwo Za Ta Taimaka Wajen Magance Rikicin Manoma Da Makiyaya — Jega
Yayin wani taro da gwamnati ta shirya domin jin ra’ayoyin jama’a a Jihar Kaduna, ministan ya ce lokacin da Shugaba Tinubu ya hau mulki, aikin bai kai kashi 15 cikin 100 ba da aka kammala.
Ya ce yanzu an kai kashi 53 cikin 100 na aikin.
A shekarar 2024, gwamnatin ta ce ta samu rancen kuɗi daga wani bankin kasuwanci na ƙasar China domin kammala aikin.
Sai dai tsawon lokacin da aikin ya ɗauka yana tafiyar hawainiya ya haifar da rashin tabbas a zukatan mazauna Kaduna da Kano.
Wasu na ganin an siyasantar da aikin wanda hakan ne ya sa aikin ba ya sauri.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp