CRI Hausa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home DAGA BIRNIN SIN

Za A Kawar Da Ta’addanci A Jihar Xinjiang Sakamakon Wadata Da Zaman Karko

by CRI Hausa
December 7, 2019
in DAGA BIRNIN SIN, DAGA TEBURIN EDITA
2 min read
Za A Kawar Da Ta’addanci A Jihar Xinjiang Sakamakon Wadata Da Zaman Karko
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG a a yau Asabar ya gabatar da wani sharhi mai taken “Za a kawar da ta’addanci a jihar Xinjiang sakamakon wadata da zaman karko”.

Sharhin ya ce, a ‘yan kwanakin da suka wuce, majalisar wakilan kasar Amurka ta shafa kashi kan ayyukan kasar Sin na yaki da ta’addanci da masu tsattsauran ra’ayi, amma zaman karko da wadata da aka samu a jihar Xinjiang ta kasar Sin sun kasance abubuwan shaida ne masu karfi wajen fallasa karyar Amurka, ko shakka babu wasu ‘yan siyasar Amurka ba zasu yi nasara ba a yunkurinsu na hana ci gaban kasar Sin ta hanyar amfani da batun Xinjiang.

Sharhin ya nuna cewa, bisa tushen koyon fasahohin da kasa da kasa suka samu wajen yaki da ta’addanci, kasar Sin ta dauki jerin matakan yaki da ta’addanci na yin rigakafi a Xinjiang. Gwamnatin jihar Xinjiang ta kafa cibiyoyin bada ilmi da horo kan sana’o’i, da nufin ceto mutanen da aka yiwa tasiri sakamakon ta’addanci da nuna tsattsaraun ra’ayi, kana da samun kwarewar fasahohi, hakan zai basu damar shiga zaman al’umma yadda ya kamata. Bisa matakai masu amfani da aka dauka, ba a samu hare haren ta’addanci ba a cikin shekaru 3 da suka gabata a jere, a cikin watanni 10 na farkon shekarar bana, adadin mutanen kasar Sin da na kasashen ketare da suka je yawon shakatawa a Xinjiang ya wuce miliyan 200, wato ya karu da kusan kashi 43 cikin 100 bisa na makamancin lokacin bara, wannan ne kuma ya shaida cewa, ana samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a wurin.

Baya ga haka, sharhin ya jaddada cewa, a cikin shekaru 30 da suka wuce, matsakaicin yawan kudin shiga da mazauna jihar Xinjiang suka samu ya ninka sama da sau 100. Wata jihar Xinjiang mai wadata da zaman karko zai kara samar da alheri ga jama’ar wurin daga kabilu daban daban da yawansu ya wuce miliyan 25, tabbas ne kuma zai kawar da ta’addanci da masu tsattsauran ra’ayi da kuma haskaka hanyar bunkasuwar jihar a nan gaba. (Bilkisu Xin)

SendShareTweetShare
Previous Post

Sharhi: Mene Ne Matsala Ga Aikin Daidaita Tunani?

Next Post

Ban Taba Karbar Fansho Ba, Inji Bafarawa

RelatedPosts

Ci Gaban Kasar Sin A Fannin Fasaha Ba Ya Tsoron Danniyar Amurka

Ci Gaban Kasar Sin A Fannin Fasaha Ba Ya Tsoron Danniyar Amurka

by CRI Hausa
17 hours ago
0

Daga Bilkisu Xin A ranar 8 ga wata, ma’aikatar kasuwanci...

Takunkuman Amurka Da Birtaniya Kan Sin Sun Keta Dokokin Kasa Da Kasa

Takunkuman Amurka Da Birtaniya Kan Sin Sun Keta Dokokin Kasa Da Kasa

by CRI Hausa
17 hours ago
0

Daga CRI Hausa Tsohon Jakadan Italiya a kasar Sin, Alberto...

Masanan Sin Da Afirka Suna Fatan Za A Kara Yin Mu’amalar Al’adu Da Juna

Masanan Sin Da Afirka Suna Fatan Za A Kara Yin Mu’amalar Al’adu Da Juna

by CRI Hausa
18 hours ago
0

Daga CRI Hausa Kwalajin nazarin harkokin Afirka na kasar Sin,...

Next Post
Ban Taba Karbar Fansho Ba, Inji Bafarawa

Ban Taba Karbar Fansho Ba, Inji Bafarawa

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version