Daga Mahdi M. Muhammad
An ja hankalin rundunar Sojan saman Nijeriya zuwa ga wasu rahotannin da ke yawa a kafofin yada labarai da ke nuna cewa yarjejeniyar kwangilar da ke tsakanin gwamnatin Nijeriya da Amurka (USA) don samar da jiragen sama na ’12 A-29 Super Tucano’, wanda aka riga aka biya kudaden, yana cikin hadari saboda rashin kyan titin jirgin sama a ‘Air Combat Training Group 407 (407 ACTG)’, Kainji.
Wannan sanarwar ta fito ne daga hannun Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar, Air Commodore Ibikunle Daramola, a inda yake cewa, NAF na son bayyana cewa, rahotannin, wadanda aka ce sun samo asali ne daga maganganun da mataimakin shugaban majalisar dattawa kan Sojin Sama ya yi yayin da yake yi wa kwamitin kula da kasafin kudin na majalisar dattawa bayani game da kudirin kasafin na 2021 na NAF, wadannan magunganu duk ba gaskiya ba ne.
A halin yanzu, 6 daga cikin jirage 12 da ake tsammani an kera su kuma a yanzu haka ana daukar su don horar da matukan jirgin NAF guda 6 wadanda su ke Amurka, tare da injiniyoyi NAF 26, da masu fasaha da masu salo, wadanda su ma ke samun horo daban-daban a cikin fannin jirgin a matsayin wani bangare na tanadin yarjejeniyar.
Haka zalika, an tsara wasu rukunin ma’aikata 35 don su kasance tare da su a farkon shekara mai zuwa. Bugu da kari, wata tawaga daga Amurka a halin yanzu tana cikin Kainji wacce ke lura da gina muhimman kayayyakin more rayuwa da aka bayar a cikin Kwangilar kafin isar da jiragen.
A halin yanzu, Jirgin saman ‘407 ACTG Kainji Runway’, wanda aka yi amfani da shi fiye da adadin shekarun da aka kiyasta a matsayin tsawon karkonsa, an kebe shi don sake farfadowa. Dangane da wannan, Majalisar Dokoki ta kasa, ta hanyar majalisar dattawa da Kwamitocin majalisar kan Sojan Sama, da kuma gwamnatin tarayya suna aiki kai tsaye don samun kudade don sake farfado da su.
Gwamnatin Amurka, a nata bangaren, ta kuma ba da tabbacin isar da jirage 12 a cikin wa’adin da aka amince da su, yayin da NAF za ta ci gaba da aiki don karfafa muhimman kayayyakin more rayuwa don tabbatar da cewa za a iya amfani da jirgin nan da nan, da zarar sun iso kasar.
Don haka NAF ke son yabawa duka majalisar dattijai da kwamitocin majalisar kan Sojan Sama da sauran hukumomin gwamnatin tarayya saboda ci gaba da goyon baya da suka baiwa hukumar damar sauke nauyin da tsarin mulki ya ba ta.
Haka zalika, NAF tana godiya ga gwamnatin Amurka saboda goyon baya da jajircewa don tabbatar da nasarar aikin jirgin ‘Super Tucano’. Yayinda take godewa manema labarai bisa goyon bayan da suka saba bayarwa, NAF din tana kira da ayi taka tsan-tsan wajen kawo rahoto domin kar a tayar da hankali.