ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Taron Editoci: Tinubu Ya Nemi ‘Yan Jarida Da Yaɗa Ingatattun Labarai Don Jawo Masu Zuba Jari A Nijeriya

by Sulaiman
3 years ago
Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nemi kafafen yaɗa labarai da su taimaka wajen bada labarai da bayanai da za su kyautata matsayin Nijeriya a idon duniya ta yadda masu zuba jari za su samu ƙwarin gwiwar saka dukiyarsu a ƙasar wanda hakan zai taimaka wa cigaban tattalin arzikinta.

Shugaban ya yi wannan kiran ne a saƙonsa da Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya karanta a madadinsa a wajen buɗe Babban Taro na 19 na Dukkan Editocin Nijeriya wanda Ƙungiyar Editocin Nijeriya (NGE) ta shirya a Uyo, Jihar Akwa Ibom, a ranar Laraba.

  • Wannan Kyauta Ce Ta Musamman Daga Daliban Makarantar Sakandaren Amurka
  • Kasashen Afirka Na Cin Gajiyar Aikin Zamanintar Da Aikin Gona Na Sin

A cikin sanarwar da mai taimakawa ministan na musamman a bangaren yaɗa labarai, Malam Rabi’u Ibrahim, ya bayar a Abuja, ya ruwaito Tinubu ya na faɗin: “An san rawar da ku ke takawa a matsayin tushen farko na labarai kuma masu wayar da kan al’umma game da abubuwan da ke faruwa a fagen tattalin arziki. Don haka, bada rahotanni a kan kari waɗanda babu ƙarin gishiri cikinsu yana taimakawa ga masu sana’o’i su yanke shawarar da ta dace, kuma ya na samar da kyakkyawan yanayi don haifar da cigaban ƙasa.

ADVERTISEMENT

“Ina kira a gareku da ku samar da kyawawan labarai waɗanda za su bada ƙwarin gwiwa ga masu zuba jari kuma su jawo irin jarin da zai inganta haɓakar tattalin arziki a wannan ƙasa tamu.

“Rawar da kafafen watsa labarai ke takawa wajen samar da kyakkyawan yanayin hada-hadar kasuwanci ta na taimakawa ga daidaita harkar kasuwanci.”

LABARAI MASU NASABA

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Shugaban ƙasar ya ce samar da kyakkyawan musayar ra’ayi kan yadda za a inganta tsarin tattalin arzikin ƙasa wani abu ne da gwamnatin sa ta yi amanna da shi, kuma ya yi kira da a samu haɗin kan editocin wajen ƙoƙarin yin tattaunawa daidai da Manufar Sabuwar Alƙibla ta gwamnatin sa.

Tinubu, wanda ya yi la’akari da matsalolin da ake ciki waɗanda janye tallafin man fetur ya haifar, ya ce gwamnatin sa ta na ɗaukar duk wani mataki da ya dace don rage raɗaɗin da ake ji, ta hanyar tsare-tsare da aka yi da za su kawo sauƙi a cikin ƙanƙanen lokaci, a yayin da ƙasar ta ke jiran ta ci moriyar abin a nan gaba.

Ya lissafa wasu daga cikin tsare-tsaren rage raɗaɗin da su ka haɗa da ƙarin albashi na N35,000 a kowane wata har tsawon watanni shida, wanda ƙari ne kan albashi mafi ƙaranci na Gwamnatin Tarayya; da kafa Asusun Tallafin Ayyuka ga Jihohi don zuba kuɗi a muhimman sassa wanda zai samar da yanayin da zai bunƙasa harkokin kasuwanci, da kuma ƙaddamar da shirin sawo motocin safa-safa samfurin CNG na naira biliyan 100, masu aiki da hasken rana, da kuma kafa Kwamitin Shugaban Ƙasa don tabbatar da aiwatar da shirin.

Ya ce: “Da yake an rattaba hannu kan dokar Ɗorin Kasafin Kuɗi na 2023, mun kammala matakan da za mu bi mu fara biyan kuɗin Tiransifar Tsabar Kuɗi N25,000 ga kowane mutum a cikin mutum miliyan 15 mafi fatara da kuma gidaje waɗanda su ka fi buƙata a Nijeriya, har tsawon wata uku.

“An bada umurnin shugaban ƙasa na fitar da tan 200,000 na hatsi daga rumbunan musamman na gwamnati ga gidajen jama’a a jihohi 36 da gundumar Abuja a farashi mai rahusa, da tan 225,000 na takin zamani, da iri, da sauran kayan aiki ga manoma.”

Tinubu ya ce a dalilin faɗuwar tarbiyya da aka samu a tsawon lokaci, wanda ya jawo raguwar mutunta ƙasa, Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai ta Tarayya (FMINO) ta na nan ta na tsara sauya labarin da ake yaɗawa game da ƙasar nan ta hanyar aiwatar da wani gagarumin shirin wayar da kan al’umma wanda nufin sa ya samar da haɗin kai, kishin ƙasa, da saka shauƙin son al’adun mu a zukatan ‘yan Nijeriya.

Shugaban ƙasar ya yi kira ga dukkan editocin kafafen yaɗa labarai da su yaƙi muguwar ɗabi’ar yaɗa labaran ƙanzon kurege, da labaran yaudara, da labaran ƙarya, masu yin barazana ga al’umma, ya ce su riƙa binciken gaskiyar lamari, da bada labarai cikin hankali da natsuwa, da inganta ilimin aikin jarida da ilimin kafafen zamani.

Ya yaba wa jigogin da su ka kafa ƙungiyar ta NGE, bisa jagorancin marigayi Alhaji Lateef Kayode Jakande, wanda zaƙaƙurin ɗan jarida ne da ake girmamawa kuma har ya riƙe muƙamin Gwamnan Jihar Legas, wanda a cikin 1961, shi da wasu, su ka kafa ƙungiyar, su ka bada gudunmawa ga cigaban ƙasa ta fuskar zamantakewa da siyasa, musamman wajen ‘yanto Nijeriya daga baƙin mulki irin na soja har aka samar da mulkin dimokiraɗiyya.

Tinubu
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace
  • Sulaiman
    ’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin
  • Sulaiman
    Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi
  • Sulaiman
    Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

MASU ALAKA

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi
Labarai

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”
Ra'ayi Riga

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma
Labarai

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Next Post
Malam Rabi’u Aminu Ya Zama Sabon Babban Limamin Jere

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Sabbin Ministoci

Kafa ‘Yansandan Jihohi: Majalisa Ta Amince Da Tsarin ‘Yar Tinƙe Wajen Kaɗa Ƙuri’a 

June 24, 2026
Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

June 24, 2026
Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.