Hukumar lura da yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi hasashen cewa za a samu kaɗuwar iska mai matsakaicin ƙarfi da hasken rana daga Litinin zuwa Laraba a sassan Nijeriya.
A ranar Litinin, NiMet ta yi hasashen ƙaruwar iska mai matsakaicin ƙarfi a Arewacin Nijeriya, tare da rage ganin da bai wuce 1000m ba a yankin. A Arewa ta tsakiya, an yi hasashen ƙaruwar iska mai ɗan karfi da gani daga 2km zuwa 5km.
- Za A Shafe Kwanaki Uku Ana Zabga Ruwa Da Tsawa Daga Lahadi – Hasashen NiMet
- NiMet Ta Yi Hasashen Tsawa Ta Kwanaki 3 Daga Talata
A kudancin Nijeriya, an yi hasashen gajimare da hasken rana a safiya, yayin da ake sa ran ruwan sama mai ɗan ƙarfi tare da guguwar iska a jihohin Rivers, Cross River, Akwa Ibom da Bayelsa daga yamma zuwa maraice. A ranar Talata, za a samu yanayi makamancin haka, inda kaɗuwar iska zai ci gaba da mamaye Arewa da Arewa ta tsakiya, yayin da ake sa ran guguwar iska da ruwan sama mai dan ƙarfi a kudancin.
A ranar Laraba, NiMet ta yi hasashen ƙarin iska mai ƙarfi a Arewa tare da ganin daga 2km zuwa 5km, yayin da Arewa ta tsakiya za ta fuskanci irin wannan yanayi. A Kudancin Nijeriya, za a sami hasken rana a safiya tare da gajimare, amma daga yamma za a fuskanci guguwar iska da ɗan ƙaramin ruwa a jihohin Rivers, Cross River, Bayelsa, Lagos da Akwa Ibom.
NiMet ta gargadi jama’a, musamman masu fama da matsalar numfashi, da su ɗauki matakan kariya daga wannan yanayi mai ƙura. Haka kuma, an yi kira ga matukan jiragen sama da su nemi bayanan yanayi daga NiMet don tsara ayyukansu. An kuma shawarci jama’a da su kasance cikin shiri tare da bin umarnin hukumomin da abin ya shafa.