Ibrahim Muhammad">

Za A Yi Wa Rukunin Ajijuwa 12 A Karamar Hukumar Dala Gyara – Hon. Ladiyo

Shugaban Kwamitin bunkasa cigaban al’umma na CPC na karamar hukumar Dala, Alhaji Umar  Mamu Ladiyo ya bayyana gamsuwarsa bisa irin kyakkyawar kulawa da Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ke bai wa bunkasa cigaban ilimi a jihar Kano musamman a matakin makarantun firamare.

Ya ce, wajibi ne su mika godiya ta musamman ga Gwamnan bisa hobbasa da ya yi na sawa a gyara ajujuwa a makarantu da suka lalace a jihar Kano.

Hon. Umar ya ce, mai girma Gwamnan ya umurci ma’aikatar kananan hukumomi hukumi da hukumar ilimin bai daya su fito da ayyuka da za a gyara makarantu kuma an fito da ajujuwa da suka lalace sannan an kirawo su a matsayinsu na shugabanin kwamitin bunkasa cigaban al’umma na kananan hukumomi an basu umurnin suje su yi wannan aiki na gyara kai tsaye.

Advertisements

Ya ce, su a karamar hukumar Dala sun dace da samun gyaran ajujuwa guda 22 wanda rukunin ajujuwa 12 kenan kuma tuni sun soma aikin gyaran.

Hon. Umar ya kara jaddada godiya ga Gwamna Ganduje bisa alkawari da ya yi na cewa duk wata hudu zai cigaba da fito da ayyuka na gyara irin wadannan wannan kuma kyakkyawan tunanine da nan gaba sai an rasa wani aji da za a nuna a `ce akwai matsala a jihar Kano.

Ya kara da cewa da yardar Allah za su cigaba da yin aiki kafada-da-kafada da shugabannin kananan hukumomi da shugabannin ma’aikatan ilimi na jihar tun daga kan kwamishinan ilimi da kwamishinan kananan hukumomi da shugaban SUBEB da sakatarorin ilimi. Ya ce, dukkan yan kunshin kwamitin gudanar da aikin gyaran a karamar hukumar Dala karkashin Shugaban karamar hukumar Hon. Ali Yantandu Suna aiki tare dan cimma nasara.

Hon. Umar Mamu Ladiyo ya godewa shugaban kwamitin bunkasa cigaban al’umma na jihar Kano, Rt. Hon. Ya’u Danshana bisa irin hadun kai da gudunmuwa da ya ke ba su kuma da yardar Allah za su fitar dashi kunya gaba daya don bunkasa cigaban ilimi.

Exit mobile version