Za Mu Ci Gaba Da Fafutukar Neman Haƙƙoƙin Mu –’Yan Fanshon ABU

Daga Idris Umar, Zariya

Gamayyar ƙungiyar yan fansho ta ƙasa, reshen jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya a jihar Kaduna ta bayyana cewa zata ɗauki matakan da suka cancanta wajen ganin an biya yayan ta haƙƙoƙin su.

Wannan furucin ya fito ne daga bakin sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙungiyar Alhaji Abdulmuminu Ibrahim, a farkon wannan makon. Sabon shugaban ya farta hakan bayan jim kaɗan da kammala zaɓen wanda ƙungiyar ta gudanar a mazaunin jami’ar dake Samaru, Zarya.

A cikin jawabin nasa, bayan ayyana shi matsayin shugaban yan fanshon, Malam Ibrahim ya bayyana cewa sabbin zaɓaɓɓun shugabanin ƙungiyar zasu ci gaba da fafutikar neman haƙƙoƙin yayan ƙungiyar fanshon jami’ar tare da haɗa hannu da ƙarfe da uwar ƙungiyar ta ƙasa wajen cimma waɗannan muradu nasu.

“ta hanyar haɗin taimakon uwar ƙungiyar ta ƙasa, zamu tabbatar da ganin cewa kowanne ɗan fansho an biya shi haƙƙin sa cikin lokaci”.

“kuma da zarar mun koma ofis, kuma ayyukan mu suka kan-kama, zamu yi tsayin daka wajen ganin cewa aƙalla kaso 33 cikin ɗari an biya su ariyas-ariyas ɗin su, ba tare da wani ɓata lokaci ba”. Ya sha alwashi.

Malam Ibrahim ya ƙara bayyana cewa“ bari in ƙara bayyana muku da cewar abinda ya faru a yau babbar nasara ce ga baki ɗayan yan fanshon jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya”.

“bugu da ƙari kuma, ba zan yi nauyin baki ba wajen sanar muku dangane da almuddahanonin da suke ta’allaƙe da danne haƙƙoƙin yan fanshon ABU, ba zamu zuba ido mu bari su tafi a banza ba”.

“sun so a ce irin wannan badaƙalar ta ci gaba da gudana tare da cutar da yan fanshon mu iya son ran su. Ni kuma ina mai tabbatar muku cewa Insha Allahu irin wannnan ba zai sake afkuwa a cikin ABU ba”. Ta bakin shi.

Exit mobile version