Za Mu Fara Fallasa Ku – Gargadin Marwa Ga Masu Safarar Kwayoyi

Daga Rabiu Ali Indabawa,

Shugaban Hukumar hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), Janar Mohammed Buba Marwa (Mai ritaya), ya gargadi masu safarar miyagun kwayoyi da masu shan miyagun kwayoyi cewa hukumar za a fitar da su da su waje duk inda suke domin fuskantar sakamakon laifin da suka aikata. Marwa ya yi wannan gargadin ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake mayar da martani kan cafke wasu barayin kwayoyi guda bakwai da ke aiki da manyan rumbunan adana kaya guda hudu a dajin Ukpuje, da ke karamar hukumar Owan Yamma ta Jihar Edo.

Bayan kamun, jimillar buhu 16, 344 na tabar wiwi, masu nauyin kilo giram 233, 778, an kuma kara da bindigogi biyu da bindigogi double barrel  guda biyu. An kiyasta darajar haramtaccen maganin da aka kama a kan Naira biliyan 1.4.

Wadanda ake zargi a hannun hukumar ta NDLEA sun hada da: Emmanuel Oki, mai shekaru 62, wanda shi ne shugaban kungiyar ‘yan bangar a Ukpuje; Chief Odi Sabato, mai shekaru 42, da Bright Inemi Edegbe, mai shekara 53. Sauran su ne Gowon Ehimigbai, mai shekaru 53; sai Enodi Ode, mai shekaru 37; Ayo Oni, kuma mai shekaru 30 da Akhime Benjamin, dan shekara 43.

A cewar kwamandan hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyin na Jihar Edo, Buba Wakawa, shi ne adadi mafi yawa da rundunar ta gano. Ya bayar da ragin magungunan kamar haka: buhu 318 mai nauyin kilogiram 80 kowannensu mai nauyin 25,440kg; Buhu 15,853 na kilogram 13 masu nauyin kilogram 206,089. Ko ma dai yaya, yayin da jimillar adadin da aka kama ya kai kilogiram 2,249, wasu kuma masu nauyin kilogram 231,529 an lalata su a cikin rumbunan.

Wakawa ya danganta nasarar aikin ga sabon yanayin da sabon Shugaban kuma Babban Jami’in Hukumar, Janar Buba Marwa ya kirkira. Marwa ya yaba wa rundunar ta Jihar Edo da ta Sojojin Nijeriya da ke cikin garin na Benin, a kan goyon bayan da suke bayarwa don tabbatar da nasarar aikin, yana mai jaddada cewa za a ci gaba da irin wannan daukar matakin a duk fadin kasar.

Ya ce tare da manyan kame-kamen tabar da aka yi a filayen tashi da saukar jiragen sama na Legas da Abuja; tabar wiwi da sauransu a jihohin Nasarawa da Katsina ta hanyar Dokokin daban-daban, Hukumar ta NDLEA za ta ci gaba da fadada layinta har sai an yi nasara a yaki da haramtattun magunguna.

Exit mobile version