Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa matsalolin da suka haddasa rashin tsaftataccen ruwan sha a faɗin jihar sun haɗa da lalacewar tashoshin samar da ruwa guda 17, lalata bututun ruwan yayin gina tituna a biranen Kaduna da Zariya, da kuma bashin albashin ma’aikatan ruwa da ya kai Naira miliyan 800 da gwamnatin da ta gabata ta bari.
A cewarsa, lokacin da suka hau mulki a shekarar 2023, aikin da suka gada na bunƙasa samar da ruwa bai kai kashi shida cikin ɗari ba, amma a halin yanzu an kai kashi talatin.
- Zhao Xintong Ya Zamo Dan Nahiyar Asiya Na Farko Da Ya Lashe Gasar Snooker Ta Kasa Da Kasa
- ‘Yansanda Sun Kama Matashi Kan Zargin Kashe Mahaifinsa Har Lahira A Jigawa
Ya ce gwamnatin ta biya bashin albashin ma’aikatan da ke aikin samar da ruwa, tare da kashe Naira miliyan 400 wajen gyaran bututun rarraba ruwa zuwa wuraren da jama’a ke zaune.
Gwamnan ya bayyana cewa sun riga sun yi odar dukkanin kayan aikin da ake buƙata daga ƙasashen Turai kuma suna kan hanyarsu zuwa Kaduna.
Ya buƙaci al’ummar jihar da su ƙara haƙuri saboda kafin ƙarshen wannan shekara, babu ƙaramar hukumar da za ta kasance ba tare da tsaftataccen ruwan sha ba.
Jihar Kaduna na ɗaya daga cikin jihohin Nijeriya da ke fama da matsalar samun tsaftataccen ruwan sha, musamman a karkara, inda mutane da dama ke fuskantar wahala wajen samun ruwan da zai ishe su sha da amfani.
Sai dai gwamnatin ta ce ta ƙudiri aniyar magance wannan matsala domin inganta rayuwar al’umma da kare lafiyar jama’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp