Zababbun Sanatocin da suka fito daga Arewa ta Tsakiya a karkashin jam’iyyu daban-daban, sun nuna rashin amincewa da mukaman shiyya da jam’iyyar APC ta sanar.
APC a shirin da ta yi, ta sahale wa Sanata Godswill Akpabio da ya fito daga shiyyar Kudu Maso Kudu ya zama shugaban majalisar dattawa a majalisar ta 10, inda kuma Sanata Barau Jibrin, daga Arewa Maso Yamma zai zama mataimakinsa.
- ‘Yansanda Sun Hallaka ‘Yan Bindiga 3, Sun Kwato Bindigogi A Zamfara
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3 A Benuwe
Haka zalika, a majalisar wakilai kuwa APC ta sahalewaTajudeen Abass daga Arewa Maso Yamma da ya zama shugaban majalisar wakilai, inda Benjamin Kalu daga Kudu Maso Gabas zai zama mataimakinsa.
Hakan ya tilasta wa zababbun Sanatocin da suka fito daga Arewa Maso Tsakiya rubuta wa shugaban APC na kasa Abdullahi Adamu wasika, inda suka sanar masa da kin lamunta da matsayin na APC ta kasa.
Sun bayyana cewa, a cikin wannan tsarin, ba a sanya Arewa ta Tsakiya a ciki ba duk da cewa zababben shugaban kasa da mataimakinsa, ba daga shiyyar suka fito ba.
Wasikar mai taken: matsayar da yan majalisa suka cimma kan shugabancin majalisa ta 10 kan shugabancin shiyya.
Sanatoci 18 ne suka rattaba hannu kan wasikar wadanda suka hada da, Sanata Mohammed Sani Musa daga Neja ta Gabas, Sanata Ashiru Oyelola Yisa daga Kwara ta Kudu, Sanata Sadiq Umar Suleiman daga Kwara ta Arewa, Sanata Mustapha Saliu daga Kwara ta Tsakiya da kuma Sanata Isah Jibrin daga Kogi ta Gabas.
Sauran su ne, Sanata Abba Moro daga Benuwe ta Kudu, Sanata Godiya Akwashiki daga Nasarawa ta Arewa, Sanata Ahmed Aliyu Wadada daga Nasarawa ta Yamma, Sanata Ireti Kingibe daga Birnin Tarayya, Sanata Sunday Karimi Steve daga Kogi ta Yamma, Sanata Sadiku Abubakar daga Kogi ta Tsakiya da kuma Sanata Peter Ndalikali Jiya daga Neja ta Kudu.
Har ila yau, sun kuma hada da Sanata Napoleon Binkap Bali daga Filato ta Kudu, Sanata Mwadkion Simon Davou daga Filato ta Arewa, Sanata Diket Plang daga Filato ta Tsakiya, Sanata Mohammed O. Onawo daga Nasarawa ta Kudu, Sanata Emmanuel M. Udende daga Benuwe ta Gabas da kuma Sanata Titus Tartenger Zam daga Benuwe ta Yamma.
Wasikar ta ce, mu Sanatocin da muka fito daga Arewa ta Tsakiya mun gudanar da ganawa a ranar 8 ga watan Mayu 2023, inda a ganawar ne, muka cimma wannan matsaya, cewar shiyyarmu ta jima tana tabbatar da ci gaban siyasa a kasar nan kuma za ta ci gaba da yin hakan tare da ci gaba da goya wa zababben shugaban kasa baya.
A cewar wasikar shiyyar ta kuma samawar wa APC kuri’u kashi 41 a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabirairu, saboda haka, ita ma shiyyar lokaci ya yi da za a rama mata.
Bisa wadanan hujojin, muna kira ga APC ta kasa da ta gaggauta janye matsayar da ta cimma kan tsarin mukaman shugabancin majalisar ta 10.