A ranar Lahadi ne dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin wanda zai yi masa takarar mataimaki a zaben 2023.
Sai dai zabin nasa ya yi fami na gyambon ciwo ga wasu gwamnoni da mabiya a arewa maso yamma.
- 2023: Ka Kula da Lafiyarka, Kwankwaso Ga Tinubu
- Ku Kara Kaimi Wajen Inganta Tsaro – Buhari Ga Shugabanni Tsaro
Tun farko a jam’iyyar APC an shiga tsilla-tsilla kan wane ne ya fi dacewa ya yi wa Tinubu takarar mataimaki, lamarin da ya kai ga dan takarar daukar Kabiru Ibrahim Masari a matsayin mataimaki na wucin gadi.
Sai dai shi ma, Masarin ya yi murabus daga mukamin nasa gabanin bayyana daukar Shettima da Tinubu ya yi.
Sai dai wannan hukunci na Tinubu bai yi wa da dama dadi ba, ganin cewar suna da yakinin gwamnonin arewa maso yamma na muhimman mutanen da zasu iya cike masa wancan gibi.
Wasu magoya baya na ganin cewar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje na iya zama mataimakin Tinubu a zaben 2023, duba da irin gudunmawar da ya ba shi.
Wasu na ganin Ganduje yayi bajinta sosai tun farkon fara tafiyar Tinubu ta nuna son yi takarar shugaban kasa, inda suke da yakinin cewar gwamnan na Kano, na da gogewa da kuma duk abin da ake bukata sama da zabin na Tinubu (Shettima).
Wasu kuma na ganin cewar gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, shi ne zabin da zai sa APC ta jijjiga jam’iyyar adawa ta PDP a babban zaben 2023.
Da fari wasu sun fara kiraye-kirayen da Tinubu ya dauki gwamnan na Kaduna, sai dai ba a san me ya faru aka haihu a ragaya ba.
A tunani irin na wadancan masu son Tinubu ya dauki El-Rufai, sun bayyana cewar gwamnan ya zama zakaran gwajin-dafi idan aka kwatanta shi da duk gwamnonin Nijeriya, wajen sanin salon shugabanci da kuma kware wajen sarrafa ayyukan ci gaba, musamman idan aka yi duba da yadda ya sauya fasalin birnin tarayya Abuja, lokacin da ya rike mukamin minista.
A wani kaulin kuwa, wasu masu sharhin siyasa na ganin Badaru Abubakar na jihar Jigawa, na iya zama mataimakin takarar Tinubu.
Wannan tunani nasu ba zai rasa nasaba da irin gudunmawar da a gwamnan na Jigawa ya bayar wajen farfado da jam’iyyar daga gargarar mutuwa a lokacin da ta ke fama da rikice-rikicen cikin gida ba.
Gwamnan na daga cikin mambobin kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar karkashin jagorancin Mai Mala Buni.
Har ila yau, suna ganin janyewa Tinubu takarar shugaban kasa da gwamnan yayi a zaben fidda-gwanin APC, wannan ma wata alama ce da ke nuni da dacewar a zabe shi.
Sai dai duk da wannan kiraye-kiraye da wasu ke yi na zabar daya daga cikin gwamnonin na arewa maso yamma bai yi tasiri ba, domin kuwa Tinubu ya kunnen uwar shegu da su.
Tsohon gwamnan na Legas, ya zabi shugaban yakin neman zabensa na takarar shugaban kasa.