Ammar Muhammad" />

Zabe: Atiku Ya Yi Watsi Da Sakamakon, Ya Garzaya Kotu

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, wato Atiku Abubakar ya yi watsi da sakamakon zaben da hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC ta sanar, inda ya ce; zai kalubalanci sakamakon a kotu.

Atiku ya bayyana hakan ne a takardar da ya sakawa hannu a yau Laraba ya kuma fitar a birnin tarayya Abuja. Inda ya ce; a bayyane yake cewa an yi murdiya a sakamakon zaben wadansu jihohin kasarnan.

INEC dai ta ce; shugaba Buhari ne ya lashe zaben shugabancin kasar da aka yi.

Buhari ya lashe da kuri’u 15,191,847 a jihohi 19 yayin da  Atiku Abubakar, ya samu kuri’u 11, 255,978 a jihohi 17 tare da birnin tarayya Abuja. Sai dai jam’iyyar PDP ba su sanya hannu a sakamakon zaben ba.

Abubakar ya ce; abin mamaki ne a ce jihohin da suke cikin tashin hankali da rashin natsuwa a ce sun fi jihohin da suke cikin kwanciyar hankali fitowa zabe.

Atiku ya ci gaba da cewa; “ Ta ya ya za a ce kuri’un da na samu a Akwa-Ibom, bai wuce kasha 50 ba kasa da yadda yake a 2015?”

Atiku dai ya yi zargin cewa; yadda aka murguda kuri’u a yankin da jam’iyyarsa ta PDP ta fi karfi, abin mamaki ne. Ya ce; an nuna rashin kwarewa sosai. Wanda ya ce; a matsayinsa na dan Nijeriya abin kunya ne gare shi, ya yadda cewa za a kyale haka ya auku.

Ya ce; wani rashin gaskiyar shi ne; yadda aka tarwatsa gudanar da zabe a wadansu rumfunan zabe da PDP ke da karfi a jihar Legas, Akwa-Ibom, Ribas da wadansu Jihohin. Ya ce; ba tare da hukumomi sun dauki wani mataki ba.

Atiku Abubakar ya ci gaba da cewa; amfani da karfi wurin gudanar da zaben, hatsari ne ga Dimokradiya, kuma mataki ne na koma zamanin mulkin mallaka na Sojoji.

Ya ce; wadansu jihohin irin su; Ribas, Akwa Ibom da Imo an yi amfani da karfin Soja, inda suka harbi mutane wadanda ya kamata a ce sun kare rayukansu. Ya ce; wannan abin Allah wadai ne, kuma bai kamata ko a nan gaba a sake barin hakan ta faru ba.

Atiku ya tabbatar da cewa; da a ce sahihin zabe aka gudanar, ba kawai zai kira wanda ya yi nasara bane ya tayi murna, zai ma taimaka wajen hada kan kasa da ci gaban gwamnatin. Ya ce; a don haka ya yi watse da sakamakon zaben, kuma zai garzaya kotu.

Exit mobile version