Fili na musamman da ya ke bawa kowa damar tofa albarkacin bakinsa game da abin da ke damunsa cikin zuciya daya shafi rayuwa.
A yau filin namu na tafe da bayanin Abba Abubakar Yakubu, yayin da ya bayyana abin da yake ci masa tuwo a kwarya game da zaben 2023, inda ya fara da cewa:
- Sin Ta Yi Kira Ga Al’ummar Kasa Da Kasa Da Ta Kara Mai Da Hankali Kan Batun Somaliya
- NRC Ta Dakatar Da Zirga-Zirgar Jiragen Kasa A Nijeriya Zuwa Bayan Zaben Shugaban Kasa
Kusan kowa a kasar nan, a kusa yake! Ma’ana a cikin fushi ko matsuwa yake, saboda yadda abubuwa suke tafiya a kasar nan. Hatta wadanda suka taka wani mataki a Tudun Mun Tsira da wadanda ke kusa da gwamnati, su ma ba lallai suna ganin yadda suke so ba.
Rayuwa ta zama wani iri, ‘yan Nijeriya sun samu kansu a wata irin rayuwa marar tabbas! Rashin tabbas ya zama shi ne kadai tabbas a kasar nan! Karfi da yaji talaka ya koyi wata irin rayuwa da a baya bai san da ita ba, wani ma ko a mafarki aka ce masa zai ga irin wannan sauyin yanayi zai yi musu, saboda yadda yake ganin komai na rayuwar sa na tafiya daidai da tsarin da ya shiryawa kansa.
Gwamnati a koda yaushe cewa take yi tana iyaka bakin kokarin ta don daidaita al’amura, kuma tana fitar wasu tsare-tsare na sassauta tsananin da talakan kasar nan ke fuska. Yayin da miliyoyin kudade ke sulalewa da sunan tallafin rage kaifin talauci, don tallafawa masu kananan sana’o’i da matasa marasa ayyukan yi. Sai dai ina wannan tallafi yake tafiya? Anya ana ba da shi a yadda gwamnati take ayyana bayarwa? Sana’o’in da aka ce ana koyarwa da tallafin da ake bayarwa da nufin kananan jari, suna isa ga wadanda ake nufin a bai wa? Wanne sa ido da babiya gwamnati ke yi don ta tabbatar ta cika alkawarin da ta yi wa talakawa? Abubuwa da yawa fa ba sa tafiya daidai!. Wanne darasi gwamnati da sauran hukumomin da ake baiwa alhakin raba tallafi da ayyukan jin kai suka koya daga boren da talakawa suka yi a lokacin zaman gida na Korona, inda aka farfasa rumbunan adana kayan abinci da aka shirya rabawa talakawa, amma aka karkatar da su, don biyan wasu bukatu na son rai. Wanne tabbaci ake da shi na cewa, irin haka ba za ta iya sake faruwa ba idan kunci ya yi wa talakawa yawa? Lallai ne gwamnati ta rika tanadar matakai na dakushe zargi da yawan bata mata suna da ake yi, saboda yadda wasu da ta yarda da su ta ba su alhakin isar mata da sako ba sa yin abin da ya dace.
A mafi akasarin lokuta, rijiya na ba da ruwa, amma guga tana hanawa!. Abubuwan da suke faruwa sakamakon canjin kudi da aka yi, da rashin samun wadatattun kudi na gudanar da kananan harkokin yau da kullum a wajen jama’a, ya kara tunzura jama’a suna ganin da gangan ake fito da irin wadannan tsare-tsare don a kuntata musu. A wani gefen ma har ana nuna gwamnati ko shugaban kasa a matsayin mutumin da ke jin dadin ganin talaka a cikin kunci. Duk kuwa da bayanan da ya sha yi wa jama’ar kasa kan burinsa na ganin talaka ya samu saukin rayuwa da adalci a kasar nan. Ban da matsalar tsaro da tsadar rayuwa da ake fuskanta, sauyin kudi da aka bullo da shi da rage yawan amfani da kudi a hadahadar mutane, ya kara jefa rayuwar talakawa cikin wani mawuyacin hali. Da masu kudin da talakawa kowa kuka ya ke yi, saboda tsayawar al’amura. Yayin da ‘yan siyasa ke kokarin siyasantar da tsarin wanda gwamnati ke cewa saboda ci gaban kasa ta bullo da shi. Har wadanda ke cikin Jam’iyya mai mulki ta APC kuma suke goyon bayan dan takarar jam’iyyar a matakin shugaban kasa da wasu matakai a tarayya da jihohi, suna danganta wannan canji da makircin siyasa.
A cewarsu, an bullo da tsarin a irin wannan lokaci ne don a dakushe farin jinin Jam’iyyar da kuma dan takarar da suke goyon baya, Sanata Bola Ahmed Tinubu. Dama mun san ‘yan siyasa, a koyaushe cikar burinsu su shi ne gaba da komai, kuma duk wani abu sa zai kawo musu cikas a zabe za su kawar da shi, ko da kuwa daga iyalinsu ne ko danginsu. Shi ya sa yanzu da suka ga zabe na gabatowa kuma talakawa sai tofin alatsine suke yi, nan da nan suka kwancewa shugaban kasa zani a kasuwa, suna nesanta kansu da canjin kudi, wasu gwamnoni ma har da zuwa kotu. Duk da abubuwan da ke faru na tsanantar rashin kudade da yunwa da aka shiga a kasa, sai gashi su ‘yan siyasa suna ta walwalar su, ana ci gaba da yakin neman zabe, ana lasa wa talakawa zuma a baki, don su zabe su babu tausayawa ta tsakani da Allah, sai dai ta kwadayin neman goyon baya. Har ma da masu cewa, in sun hau mulki za su soke wannan tsari kowa ya koma amfani da tsohon kudi da sabo. Su kuwa talakawa babu abin da suke yi sai murna, suna ganin don su ake kokarin kafa sabuwar gwamnati.
Koda yake, ‘yan siyasa na ganin talakawa kamar kaji suke, ana watsa musu tsaba shi kenan. Don haka sun bi sun kwashe sabbin kudade a bankuna sun boye sai lokacin zabe ya yi za su fito da su suna sayen ra’ayin talakawa, saboda a lokacin an shiga kangi, ganin sabon kudi ba, rahama ce a gun talaka, ko da nawa zai samu, ba zai damu ba, in dai ‘yan canji za su shigo hannunsa. Saboda a takure yake, iyalinsa na jiran ya nemo ya kawo gida! Duk kuwa da yadda ake samun wasu da ke cewa sun fitar da rai daga samun canji a kasar nan, ko samun shugabanni nagari, don haka ba su babu kara jefa kuri’a. Wasu kuma na ganin tun da ba son ran su shi ne zai kawo canji ba to, gara ko nawa aka ba su su karba, don su rage asara, dama can dukiyar kasa ce aka sace.
To, ni dai abin da zan gaya wa talakan Nijeriya shi ne yanzu ne lokacin da ya fi dacewa ya fita ya yi zabe, kuma ya tabbatar abin da yake so shi ya zaba ba tare da biye wa wani abin duniya ya canza masa tunani ba, ya zabi wadanda zuciyar sa ta fi natsuwa da za su kwatanta masa adalci. Ya huce haushin sa ta hanyar amfani da katinsa na zabe wajen tabbatar da ganin tsofaffin ‘yan siyasar da a baya suka yaudare shi ba su tsinana komai na kawo wa talaka sauki ba, sun yi waje, ya zabi wadanda za su iya rike amana, kuma su kawo gyara.
Mu tabbatar katinan zaben mu na kusa, ta yadda lokaci na yi za mu dauko su, mu je mu yi zabe, kuma mu yi addu’a, Allah ya sa wadanda za su hau karagar mulki a matakai daban-daban, sun zo da niyyar alheri, sun zo da shirin kawo gyara, ba arzuta kansu da satar dukiyar kasa ba.