Rundunar sojin Nijeriya ta jaddada kudirinta na hada kai da ‘yansanda da sauran jami’an tsaro domin ganin an gudanar da zaben 2023 cikin kwanciyar hankali.
Babban kwamandan rundunar sojojin Nijeriya ta 7, Manjo-Janar Waidi Shuaib ne, ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga kwamishinan ‘yansandan Jihar Borno, Abdu Umar a ranar Talata a Maiduguri.
- Ta’addanci Ya Zama Tarihi, Nijeriya Na Cikin Aminci – Lai Muhammad
- Ambaliyar Ruwa: Jihohi 21 Sun Samu Kayayyakin Agaji –Sadiya Farouq
Ya ce hada gwiwa tsakanin sojoji da ‘yansanda da sauran jami’an tsaro zai taimaka wajen samar da ingantaccen tsaro kafin zabe da kuma bayan zabe a kasar.
GOC ya ce ziyarar za ta ba shi damar kara kaimin tunani game da shirye-shiryen ‘yansanda don magance matsalolin tsaro a lokacin zabe.
“Hukumar ‘yansanda ita ce kan gaba amma saboda yanayin yankin Arewa-maso-Gabas ke ciki, ya bukaci sojoji da su jagoranci ayyuka daban-daban.
“Rikicin zabe na iya faruwa ko dai kafin gudanar da zabukan, ko a lokacin a lokacin zabe ko bayan zabe, kuma dukkanin hukumomin biyu za su hada hannu wajen magance wadannan matsalolin.
“Kamar yadda aka fara yakin neman zabe, jami’an tsaro na hadin gwiwa sukan gudanar da ayyuka don tabbatar da cewa babban birnin ya kasance lafiya.
“Za mu so mu tabbatar da kuma karfafa dukkan sojojinmu ciki har da rundunonin sojan hadin gwiwa domin samun ingantaccen muhalli a cikin birnin Maiduguri.
“An samj rahoton sirri da yawa. Sai dai idan muka yi aiki tare za a tabbatar da cewa abubuwa sun tafi yadda suka dace,” in ji shi.
Da yake mayar da martani, Abdu ya ce ‘yansandan za su ci gaba da hada kai da sojoji domin kare rayuka da dukiyoyi a jihar.
Ya ce rundunar ta karfafa sintiri tare da hadin gwiwar rundunonin sojoji domin yaki da miyagun laifuka a cikin babban birnin Maiduguri.
Kwamishinan ya sake nanata shirye-shiryen ‘yansanda na samar da tsaro domin saukaka gudanar da zabe cikin gaskiya.