Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa jimillar ‘yan Nijeriya 4,567,689 za su raba gardama a zaben cike gurbi da zai gudana a watan Fabrairun a jihohi 27.
A cewar sanarwar gabanin zabe da babban sakataren yada labarai na INEC, Mista Rotimi Oyekanmi ya fitar, ta bayyana cewa a cikin adadin, mutum 2,189,171 ne za su raba gardama a zaben cike gurbi a mazabun ‘yan majalisar dattawa guda biyu da kuma mazabu hudu na ‘yan majalisar wakilai da za su gudana a jihohi uku.
- Za A Kulle Miliyoyin Asusun Banki Saboda Rashin Katin Dan Kasa
- NERC Ta Kori Dukkan Daraktocin Wutar Lantarki Na Jihar Kaduna
Sanarwar ta ci gaba da bayyana cewa masu zabe 2,220,912 bisa umurnin kotu za su yi zaben cike gurbi na ‘yan majalisar tarayya, yayin da masu kada kuri’a 157,606 za su gudanar da zaben ‘yan majalisar jihohi.
Zaben cike gurbin zai gudana ne a mazaben ‘yan majalisar dattawa guda biyu a kudancin jihohin Ebony da kuma Yobe ta gabas, yayin da za a gudanar da zaben a mazabu hudu na majalisar wakilai a jihohin Kebbi, Legas, Ondo da Taraba da kuma wasu mazabu uku da ke Benuwai da Borno da Kaduna.
An dai samu wadannan gurbi ne sakamakon ajiye aiki da kuma mutu na wasu ‘yan majalisa.
Haka kuma sanarwar ta ce za a gudanar da zaben cike gurbi a mazabar dan majalisa guda daya a Jihar Filato bisa hukuncin kotu da kuma wasu mazabu na tarayya guda 12.
Mazaun ‘yan majalisa da za a gudanar da zaben sun hada da Surulere da ke Jihar Legas, Gauri/Shanta/Ingaski da Arewa/Dandi da suke cikin Jihar Kebbi, Arewa maso gabas da Arewa maso yamma na Akoko da ke Jihar Ondo, Jalingo/Yorro/Zing a Jihar Taraba, Ikono/Ini a Jihar Akwa Ibom da kuma Akamkpa/Biase da ke Jihar Kurus Ribas.
Sauran sun hada da Arewacin Nnewi da Kudancin Nnewi da Arewacin Orumba da kudancin Orumba na Jihar Anambra, Arewacin Igbo Eze da Udenu a Jihar Inugu, Birnin Kudu da Buji da ke Jihar Jigawa, Igabi da Kachiya da Kagarko a Jihar Kaduna, Faskari/Kankara/Sabuwa na Jihar Katsina, Arewacin Jos da Bases a Jihar Filato da kuma Fine da Fune da ke Jihar Yobe.
Haka kuma za a gudanar da zaben ‘yan majalisar dattawa a yammacin Yobe da Filato ta tsakiya bisa hukuncin kotu.
Sannan a matsaki na jiha kuwa, za a gudanar da zaben cike gurbi a jihohin Adamawa, Akwa Ibom Bauchi, Bayelsa, Kurod Ribas, Delta, Inugu, Kaduna, Kano, Nasarawa, Neja, Oyo, Sakwato, Zamfara, Benuwai da kuma Borno.
Za a mika sunayen ‘yan takarar zaben cike gurbi ga hukumar zabe a ranar 13 ga watan Janairu. Sannan za a fitar da sunayen ‘yan takara na karshe a ranar 17 ga Janairu.
Haka kuma za a fara gudanar da kamfen tun daga ranar 18 ga Janairu, sannan za a rufe yakin neman zabe a ranar 1 ga watan Fabrairun 2024.