Idris Umar" />

Zaben Fidda Da Gwani Na Jam’iyyar APC Ya Gagara A Karamar Hukumar Sabon Gari Zariya

Daga Idris Umar, Zariya

Zaben fidda da dan takarar da wakilci jam’iyyar APC a zaben kananan hukumomin dake tafe a jihar Kaduna ya guda a fadin jihar ranar Asabar 24 ga watan 24 ga watan Maris amma zaben ya gagara a karamar hukumar Sabon Gari domin rashin daidaito da sulhu a tsakanin manyan ‘yan takara su biyu da Injiniya Muhammad Usaman da Alhaji Yusuf Salihu Shaka.

Karamar hukumar Sabon Gari na daya daga cikin kananan hukumomin da aka sami tangarda da takai ga kasa yin zaben kirikiri duk da cewa kowa ya hallara daga dukkan bangarorin ‘yan takaran da jami’an jam’iyyar na karamar hukumar da jihar.

Tun da sanyin safiya ranar asabar din zaben ne magoya bayan ‘yan takaran suka taru a filin wasa na Dogarawa da ke babban titin zuwa Kano domin tantancewa da kada kuri’a.

Bayan kowa daga bangaren ‘yan takaran ta kujeran ta karamar hukumar sun hadu tare da malaman zabe baki daya kuma dukkanin ‘yan takarar sun sami halattar. Bayan yan mintuna kadanne sai kacaniya ta sarke a tsakanin wakilan yan takarar guda biyu.

Kacaniyar ta barke ne bisa wasu abubuwa ne da  ake zargi da cewa wani bangaren ne ke neman su tabka magudi.

Wanda hakan yasa lamarin zaben ya fada walawala bisa haka ne masu kada kuri’u da yawa suka fice dakin wasan.

Wakilinmu  ya nemi jin ta bakin ‘yan takarar guda biyu amma lamarin ya cutura.

Bayan barin gurin zaben ne sai wakilinmu ya nemi jin ta bakin jami’an gudanar na kamfen na Honorabul Mohammad Usman Maku wato Alhaji Mai Zinaru amma ya tabbatar wa wakilinmu cewa ba zai ce komi ba.

Shiko Kwamred Isa Falladan na bangaren dan Tara Honorabul Yusuf Shaka in da ya ce, su sam basu yarda da abin da ya faru ba na  kin yin zabe a wannan karamar hukumar bisa wasu dalilai da wasu suka kawo da bai dace na don haka ya ce, suna kira ga uwar jam’iyya dasu sani cewa, ba ayi zabe ba a karamar hukumar Sabon Sari don haka suna kira da a bubi lamarin kuma a dauki matakin daya dace.

Injiniya Gago Shima yana daya daga cikin magoyan bayan Honorabul Yusuf Shaka, ya yi godiya ne ga jama’ar karamar hukumar Sabon Gari game da kauna da suka nuna wa maigidan sa a wannan rana ya ce, duk da cewa ‘yan hana ruwa gudu sun yi abin da suka ga dama na dakile gaskiya a fili kuma ya kuma mika godiya ga mai girma gwamnan jihar Kaduna bisa kokarinsa na kawo hadin kai a jihar ta Kaduna, ya ce, suna kira ga jama’ar su da kasance cikin shiri amsar hukuncin da uwar jam’iyya za ta kawo a kan zaben da ba a yi ba a karamar hukumar su.

Exit mobile version