Muhammad Maitela">

Zaben Gwamna: Yadda ‘Yan Takara Uku Suka Fafata A Ondo

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa yan takara daga jam’iyyun siyasa 17 ne su ka shiga zawarcin kujerar gwamnan jihar Ondo a zaben da ya gudana ranar Asabar ta 10 ga watan 10- 2020.

Yayin da ma su zabe daga kananan hukumomi 18 ne daga shiyyoyi uku a fadin jihar Ondo za su yanke hukuncin zabar daya a tsakanin wadannan yan takara 17, a matsayin sabon gwamnan jihar.

Bugu da kari kuma, zawarcin shiga fadar gwamnatin jihar dake Alagbaka zai gudana a tsakanin manyan yan takara uku da suka yi fice, daga sassa uku a jihar wadanda kuma duk lauyoyi ne.

Advertisements

Wadanda su ka hada da Rotimi Akeredolu, Eyitayo Jegede hadi da

Agboola Ajayi, daga manyan jam’iyyun siyasa a jihar na APC, PDP) da  Zenith Labour Party (ZLP).

A gefe guda kuma, a wannan zaben gwamnan jihar Ondo zai gudana a rumfunan zabe 3,009 da gundumomi 203 a fadin wadannan kananan hukumomi 18 a jihar.

A hannu guda kuma, wasu rahotanni daga rundunar yan-sandan jihar ta bayyana cewa an samu hatsaniya a wasu rumfunan zabe na Edo Lodge 11 da ke Oke Ijebu a Akure a lokacin zaben

Kamar yadda jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan Ondo, Mista Tee-Lee Ikoro ya tabbatar wa manema labarai a Akure.

Ya ce hatsaniyar wadda ta jawo takaddama ta hanyar harbe-harben nindigigi ta kan mai uwa da wabi, tare da shaidar da cewa babu rasa rayuka a rikicin.

Bugu da kari kuma, Tee-Lee Ikoro ya tabbatar da cewa rundunar ta aike da jami’an ta domin ganin kwantar da kurar rikicin.

Haka kuma rundunar ta bayyana damke wani mutum da ta ke zargi da aikata magudi ta hanyar sayen katin zabe ga hannun jama’a, a lokacin zaben. Mutumin wanda ya nuna kansa a matsayin mai sanya ido a zaben a gunduma ta 4, a rumfar zabe ta Shagari Market (Unit 15), da ke kan babbar hanyar Owo zuwa birnin Benin.

A nashi bangaren kuma, jami’in kula da zaben gwamnan jihar Ondo- Dr. Emeka Onanamadu, ya yaba da yadda zaben ke gudana cikin tsanaki.

Jami’i mai sanya ido a zaben jihar a yankunan Owo, Ose da Akoko a kudu maso yammacin jihar Ondo, ya yaba yadda zaben gwamnan ke gudana cikin tsanaki a yankin.

Ya bayyana hakan ga manema labarai a sa’ilin da ya ziyarci rumfar mazabar Ijebu II (Unit 006), gunduma ta 5. Yayin da ya ce, ”mun yaba da yadda ma su zaben ke jefa kuri’un su a tsanake kana da yadda jami’an tsaro ke aikin tabbatar da tsaro a lokutan zaben.”

Mista Ononamadu ya kara da cewa, jama’a sun fito sosai don kada kuri’un su, tare da bayyana cewa hakan ya nuna zaben zai kammala ba tare da wata tangarda ba.

“Har wala yau, zancen da nake daku ba mu samu rahoton wata tashin-tashina ba. Al’amura su na tafiya bisa tsari a duk inda mu ka ziyarta, kuma mu na kyautata zaton haka zaben zai gudana har zuwa karshen sa.” In ji shi.

A gefe guda kuma, a nashi bangaren, daya daga cikin masu sanya ido a zaben- Mista Deji Adeyanju, ya bayyana gamsuwar sa dangane da yadda zaben ke gudana.

“Haka kuma yadda masu jefa kuri’a ke gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da limana abin burgewa ne, haka kuma muna burin abin ya ci gaba da gudana a haka; kuma idan hakan ya samu babu wata matsalar da za a fuskanta har zuwa karshen zaben.”

Mista Adeyanju ya kara da yaba wa da yadda zaben ke gudana tare da yadda hukumar ta raba ma’aikata da kayan zaben cikin lokaci, haka kuma da kokarin jami’an tsaro tare da samun hadin kan shugabanin Jam’iyyun siyasa da masu ruwa da tsaki.

A daidai lokacin da muke hada wannan rahoton, hukumar zabe mai zaman kanta ta na kokarin harhada alkaluman zaben daga kananan hukumomi da gundumomi a jihar.

 

 

Ci gaba da shafi na daya

Kudurin ya kuma zartar da hukuncin sauke Dagacin garin Zadawa, Ibrahim Yusuf Atiku daga kujerar sa ta mulki bisa rarraba dazuzzuka da ya yi yana karbar kudade daga wuraren wadanda ya rarrabawa daji, tare da damke shi nan take, domin ya fuskaci hukucin hukuma bisa tabargaza da ya aikata.

“Ya kuma zama wajibi wa masarautar Misau ta tabbatar da cewa, Ibrahim Yusuf Atiku bai nemi zama Dagacin garin Zadawa ba, a duk lokacin da kujerar mulkin ta Zadawa ta kasance babu kowa a kanta.”

Kudurin ya kuma zartar da hukuncin baiwa magadan wadanda suka rasa rayukan su a cikin rikicin na kauyen Zadawa, kudaden taimako, dama wadanda aka yi jinyar su a asibiti sakamakon rikicin, hadi da wadanda suka yi hasarar dokiyoyin su dangane da rikicin.

Kudurin ya kuma lura da cewar, za a iya hana faruwar wannan tashin-tashina na tsakanin manoma da makiyaya, matukar an bi sharudda da zayya-nannun dokoki na gandun daki, da kuma dokoki na gwamnati wadanda suka tsara hanyoyin mallakar dazuka da makaman-tansu.

Gwamnatin jihar Bauchi ta ji takaici matuka yadda ake take dokoki da sharuddan mallakar gonaki a gandun daji ko dazuzzukar ta, da kuma wakaci-ka-tashin dazuka da ake yi, da yake dakushe ‘yanchin Fulani makiyaya na kiwata dabbobin su.

Dangane da rashin bin ka’ida na mallakar daji ko gonaki daga hannun gwamnati, an soke dukkan wata takadar gona ko gandun daji da mutane suka yi a baya, ba bisa ka’ida ba domin wanzar da zaman lafiya tsakanin jama’a, kuma daga yau, gwamnati za ta yi ba sani ba sabo ga duk wanda ya ketare iyaka kan lamuran gonaki da gandun daji a cikin kowace karamar hukuma.

Gwamnati a fayyace tana baiwa daukacin jama’ar ta tabbaci na kare dazuka da labuka na gandun dazukar ta, hadi da kebabbun dazuzzuka, da gonaki ta yadda za a samu wanzuwar zaman lafiya tsakanin al’ummomi dabam-dabam dake daukacin fadin jihar Bauchi.

Exit mobile version