Rundunar ‘yan sandan Jihar Legas ta sha alwashin gurfanar da masu yada labaran karya da masu aikata barna a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Benjamin Hundeyin, ya fitar a ranar Litinin.
- Ka Daina Gararamba A Titi Ka Tafi Kotu —Martanin APC Ga Atiku
- Tinubu Ya Yi Allah Wadai Da Harin Zamfara Da Kano
A cewarsa, rundunar ba ta da masaniya game da munanan kalamai, tada hankali da tada zaune tsaye da ake yadawa a ko ina a shafukan sada zumunta da nufin haifar da firgici, rashin jituwa da hargitsi a jihar.
“Hukumar ta fara binciken wannan abin tsoro da nufin kamawa tare da hukunta wadanda aka samu da laifi.
“An yi kira ga mutanen kirki da mazauna jihar da su yi watsi da duk wani nau’i na sakonni, musamman a shafukan sada zumunta na yanar gizo da ke nuna labaran karya da yaudara da nufin kawo cikas ga zaman lafiya da ake samu a jihar,” in ji Hundeyin.
Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Idowu Owohunwa, ya tabbatar wa da masu zabe cewa, rundunar ta yi shiri domin tabbatar da zabe mai inganci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp