Yayin da jama’a ke nuna rashin jin dadinsu kan hukuncin da wasu alkalan kotunan daukaka kara suka yi a kan zaben Gwamnan Jihar Kano, majalisar kula da shari’a ta kasa (NJC) ta fara daukan matakai kan wannan lamarin.
Na farko daga cikin alkalan da suke fuskantar tuhuma daga NJC shi ne, mai shari’a Moore Aseimo Abraham Adumein na kotun daukaka kara wanda ya zartar da hukunci mai cike da ce-ce-ku-ce a shari’ar gwamnan Jihar Kano.
- Gwamnatin Kaduna Ta Kaddamar Da Kwamitin Mutum 8 Don Inganta Harkokin Aikin Hajjin 2024
- Da Dumi-dumi: Kotun Daukaka Kara Ta Ayyana Ranar Yanke Hukunci Kan Kujerar Gwamnan Adamawa
LEADERSHIP ta ruwaito cewa mai shari’a Adumein yana fuskantar tuhuma saboda gazawarsa wajen ganowa da kuma kyara kura-kuran rubutun da aka yi a shari’ar Gwamnan Jihar Kano.
Wata majiyar ta ce da yawa daga cikin ‘yan Nijeriya sun yi korafi kan hukuncin shara’ar gwamnan Kano, wanda har yanzu suke bukatar yi musu bayanin yadda aka samu kura-kuran.
“Yawancin ‘yan Nijeriya da ke magana a kan hukuncin ba su karanta ba. Kuskuren da aka samu a hukuncin ya nuna karara kuskure ne na alkali amma ba na yi masa uzuri ba, dole ne ya amsa kuskurensa saboda jahilci ba uzuri ba ne a shari’a, dole ne ya fuskanci hukunci a wuyansa.
“Kuskuren wannan hukuncin ya fito ne daga magatakarda wanda ya yi aiki a kai. Alkalin bai karanta karshen hukuncin ba bayan da sakatare ya yi aiki a kai. Alkalin da sakataren da suka yi aiki a kai dole ne su fuskanci hukunci,” in ji majiyar.
Majiyar ta ci gaba da cewa a bangaren shari’a tafka kuskure babban abin kunya ne ba kamar sauran sass aba, shi ya sa kuskure ke zama babban laifi idan an aikata a bangaren.
Ya ce NJC ba ta kare alkalan ta da aka samu da laifin ko kuma kuskure wajen gudanar da aiki. Majiyar ta ce, “Kusan kashi 98 cikin 100 na koke-koken da ake yi wa alkalan ana gudanar da bincike sannan idan aka same su da laifi za a iya dakatar da su ko kuma a kore su daga aiki.
“Majalisar NJC tana biyan dukkan alkalan tarayya albashinsu, shi ya sa muke samun horo idan aka same su da laifi. NJC kamar kotu ce ga alkalai, saboda masu korafi da alkalai suna wakiltar lauyoyi ne, inda ake tafka muhawara a dukkan wasu batutuwa.
“Bayan sun saurare su, za su yi watsi da bukatar ko kuma su sanya wa alkali takunkumi, ya danganta da hujjar da aka gabatar. Yawancin shari’o’in da ake yi wa alkalan a NJC daga kotun daukaka kara suke tasowa.” In Ji majiyar