Connect with us

LABARAI

Zai Wuya Dalar Gyada Ta Dawo A Kano Saboda Samun Habakar Noma -Babawa

Published

on

An bayyana Dalar gyada da aka tabayi a baya a jahar Kano wanda yanzu karuwar al’umma da bunkasar noma  da samar da sabbin tsare-tsare na ma’ajiyar kayan amfanin gona yasa babushi ya zama wani abune kawai na tarihi  dake nuna alamar  yanda Kano ta tunbatsa kafin samun canjin zamani da yanzu bai kamata a rika tunanin bacewarsa ko dawo dashi ba.Shugaban Kanfanin hada-hadar kayan amfanin Gona na “Babawa Nigeria Limited”Alhaji Garba  Hamza Babawa ya bayyana haka da yake zantawa da wakilimmu a wani taronda ake  na masu ruwa da tsaki akan harkar noma da hada-hadar kayan gona da sarrafashi  a babban dakin taro na dakin karatu na Murtala Muhammed dake Kano.

Yace tsarin ma’ajiyar da ake dashi na manyan gine-gine da ake kira “ware-house”a yanzu ya nunkin tsarin baya na tsibe kaya da ake  ta tsarin yin Dala dashi.Wannan tsari na zamani akwai tsaro da inganci ta ajiye kayan a killace a waje daya,wanda a baya fili ake samu fetal a tara kayan abinci musamman gyada a tsibe a rufe da tampol.Amma yanzu  zamani yazo da canji ana yin manyan dakuna na ajiya wanda yake bada kariya  ta tsaro da kariya daga ruwa  da kariya daga kwari.

Alhaji Garba Hamza Babawa yace yanzu wannan yafi inganci,da ace ana Dalar kayan a yanzu,yanda ake  ajiyewa a waje a halinda  ake ciki na yawaitar  rashin gaskiya a cikin al’umma in akace tara kayan ake a waje  sai kaga wasu maha’inta suna zuwa suna sacewa.Lokaci ya wuce yanzu da za a rika tunanin a dawo da Dalar gyada ,duk da baci baya bane, amma yanzu idan akayi la’akari da yanda ake noma sosai fiye da  da,kuma mutane yanzu sun nada yawa.Gonaki sun karu da  yawa ana ma maida wasu dazuka gonakin, yanzu abubuwa da ake nomawa na nau’in kayan abinci suna karuwane.

Yayi nuni da cewa a baya bai wuce a noma dawa gero, wake da gyadar ba,amma yanzu ana noma shinkafa wacce tama zama itace abinci da akafi mu’amala da ita  ga alkama da sauran kayayakin gona iri daban-daban,duk da ba a ganin yawan gyada yanzu a tare a kasarnan, amma wanda ake nomawa a yanzu in aka kwatanta da baya da ake tara Dalarta ta yanzu tafi yawa.

Alhaji Garba yace yanzu irin sito-sito da ake dasu a kasuwar Dawanau da sauran wurare sai a sami sito daya kawai  yana iya daukar abinda ada ake tsibewa a lokacinda ake Dalar gyada daya ,yanzu manya-manyan Dakunan ajiya da ake dasu na zamani yana ajiye nunki na Dalar gyada da ake a baya, saboda noma ya habaka  kuma an sami canji na tsarin adana kayan.

Shugaban Kamfanin na “Babawa Nigeria Limited” Alhaji Gaarba Hamza yace abinda Gwamnati yakamata ta rikayi, ta rika kididdige yawan mutane, sannan sai a rika kara yawan tallafin noma a duk shekara domin komai karuwa yake kullum,domin duk abinda akayi masa yawa sai aga kamar ba’ayi, duk da kuwa ana fitar da shigowa da nau’i- nau’i na kayan abinci daga waje da cikin kasarnan.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: