Kungiyar tabbatar da zaman lafiya a cikin al’umma ta kasa da kasa da ke gudanar da ayyukanta a kasar nan (SFCGN), ta rattaba hannu da hukumar wanzar da zaman lafiya ta Jihar Kaduna da kuma cibiyar hadakar addinai ta jihar.
Sun ratattaba hannun bisa nufin kara karfafa girmama addinan mabiya Musulunci da kuma na Kirista da tabbatar da zaman lafiya a cikin al’umomin jihar.
- Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Hanyar Tafiyarsu Ta Kai Hari Ga Al’ummar Jihar Kaduna
- Za A Bude Shafin Karbar Bashin Dalibai A Ranar 24 Ga Mayu
An rabbata hannun ne a taron tattaunawa na kwana daya a Kaduna.
A jawabinsa a wajen taron, mataikin shugabar hukumar wanzar da zaman lafiya ta jihar, Dakta Saleh Momale, ya ce sanya hannun zai bai wa masu ruwa da tsaki daban- daban na jihar da kananan hukumomi 23 na jihar da sauran kungiyoyin hadakar addinai da ke a jihar da sarakunna gargajiya damar ci gaba da samar da zaman lafiya mai dorewa.
Shi kuwa, Darakta Janar na hukumar cibiyar hadakar addinai ta jihar, Barista Tahir Tahir ya yi kira ga daukacin al’ummar jihar da su yi watsi da dukkan wasu bambancen da ke a tsakaninsu don a kara wanzar da zaman lafiya a jihar.
Ita ma a nata jawabin, Daraktar kungiyar SFCGN, Fatima Madaki ta ce jaddada zaman lafiya a cikin al’umma na da mutukar muhimmanci.
Shi ma jagoran tawagar kungiyar ‘yan jarida na kasa da ke wallafa labarukan zaman lafiya, Ibrahima Yakubu ya ce, taron zai bayar da damar kara karfafa zaman lafiya a tsakanin mabiya addinin Musulunci da na Kirista.