Connect with us

TASKIRA

Zaman ‘Yan Marina A Kan Wakar ‘Jaruma’ Ta Hamisu Breaker  

Published

on

“Ashe da rai nake son ki jaruma ba da zuciya ta ba,

Komai ruwa da iska a kanki ba za na daina kewa ba,

Idan na samu zarrar samunki ba za na tanka kowa ba,

Ni banga me harara ba, Balle na waiwaya ba..”

  “In dai a kanki ne za na jure wahalar zuwa garin nisa,

Da an taba ki a jira ni dan ko tilas na zo na dau fansa,

Jurumin Jiranki nai dan ki zo na kale ki gimbiyar Hausa,

Sirri na rayuwata ke ce kawai da kin kira da na amsa,

Zuma a baki dadi gare ta kin ba ni taki na lasa,

In dai a kan ki ne na yi nisa dan ba kiran da zan amsa,

Tilas ganin mu, Tilas barin mu kaunarki tun da nai nisa,

To ba batun na fasa ko za a ce mun na ba da rai fansa,

Tsarin zubinki daidai ne,

Ya kama zuciyata ne,

Na jin kawai mafarki ne,

Na sonki so mafarki ne,

Ni ban da damuwa, in har zan buda ‘yan idanuna in kallo ki ga ki dab da ni to me za ya dami kalbina…

 

Wakar Jarumar Mata kenan wadda Hamisu Breaker ya wallafa. Mawakin ya nuna fusaha da kwarewarsa wajen yin amfani da zafafan kalamai masu dadi, taushi, da burgewa gami da nishadantarwa a dausayin soyayya.

Mawakin ya kuma yi amfani da wasu kalmomi masu saurin isar da sako ta yadda salon wakarsa ta sauya da sauran mawaka, idan muka yi duba kuma muka yi nazari da baitocinsa na farko, ya yi amfani da wata kalma wadda tasha ban-ban da kalmomin da sauran mawakan zamani suke sakawa cikin wakokin su na soyayya. Mawakin da ya yi fuce a yanzu ya kuma shahara ya zaga ko ina sanadiyyar wannan wakar da kuma abubuwan da suka biyo bayanta, ya yi amfani da kalmar da sauran mawaka basa sakata cikin wakokin su na soyayya, wadda tana daya daga cikin kalaman da suka ja hankulan jama’a wajen karkatuwa da wakar.

Sauran mawaka sukan yi amfani da kalmar suna son masoyi ko masoyiya a cikin zuciya, amma shi Breaker ta wannan bangare ya bambanta fadar wannan kalmar inda ya ce “Ashe da rai nake son ki jaruma ba da zuciyata ba”, wannan babbar kalma ce wadda kuma duk wanda ya san mene so ya san kalmar an tsarata a mazaunin ta. Wakar ta yi fuce ta inda duk inda ka za ka, za ka ji ana maganar wakar ko kuma ana sauraranta, dalilin dadin wakar ya sa ta kai ga har wasu manyan mata suka yi amfani da ita wajen taka rawarsu bayan gasar haka da wata ta sanya a shafin Instagram. LEADERSHIP A Yau Juma’a ta zakulo wasu da suka san wakar da kuma kallon abubuwan da suka biyo bayan sakin wakar ta gasar rawa a tsakanin ma’aurata, inda suka fayyace ra’ayoyinsu game da wakar ta jarumar Mata. Ga kuma yadda ta kasance.

 

Wakar Tana Sa Natsuwa A Zuciya, Amma… In Ji Hauwa S. Zariya

Gaskiya wakar abar soce, musamman idan a ka yi la’akari da kalaman da ke dauke da shi, ba su ba duk wani wanda ya san me ake kira soyayya da zaran ya jita sai ya samu nutsuwa a zuciyarsa. Matan auren da su kai rawa da wakar a nawa ra’ayin hakan be kamata ba, musamman idan mukai duba da koyar war addinin mu sannan kuma su kansu mazajen.

Abu na farko da za mu duba, sufa wa’yan nan mazajen ba yara bane, suna da ‘ya’ya da surukai,sabida Allah yaya ‘ya’yansa zasu ji a zuciyarsu yayinda wanan bideos d,in ta riskesu? Duk da nasan da matayensu ne sukayi, wasu zasuce ba wani abu bane, eh nasan ba wani abu bane sannan kuma yin hakan be haramta ba, ammma ko addini musulci be barmu haka sakaka ba saida ya koyar damu abubuwa da dama ciki co harda sirri,ba laifi idan suyi haka Amma be kamata su yadawa duniya ba,idan har sabida Allah da manzon sa da kuma niyyar farantawa mazajen sune kamar yanda wasu ke ikrari  zaifi dacewa su adana shi kada su yadawa duniya. Misali ace kece hakan ya faru da mahaifinki yaya zakiji a zuciyarki?haka zalika suma ‘ya’yansu ba zasuji dadi’n gani wanan bideos din ba, duk kasance warsu mataye su ne. Wannan abu da suka yi zai iya zubar masu da mutunci da k’imar da ake kallonsu dashi.

 

Rawar Da Wasu Suka Yi Ce Ba Ta Dace Ba – Hajiya Maryam

Nidai gaskiya abunda zance game da wannan raye rayen da ake yi shi ne mata muji tsoron Allah soyayya ba hauka bace da za ki, fito duniya kina rawa kina daurawa a social media a matsayinki na matar aure be dace ba sabo haka mata da maza muji tsoron Allah mu koma ga Allah.

 

Maza Ya Fi Dacewa Su Taka Rawar Ba Mata Ba – Mimskueen

Assalamu Alaikum Wakar tayi dadi sosai. Amma a ganina Namiji ya kamata ya taka mun kamar yadda Namiji ne ya rera, ya yi kirarin, don haka ni ba zan taka maka ba, kai za ka taka ka nuna kana so na, “if not forget the dance” gaskiya kowa ya rike ra’ayinsa.

 

PAGE 15

Allah Ya Kara Basira, Hamisu Breaker – Aisha Shehu

Assalamu alaikum sunana Aisha Shehu Maman twins, gaskiya babu abinda zance sai dai ince wakar Hamisu ta yi ma’ana kuma ta bada abubuwan da ake so musamman ga masoya,tunda gashi tsofaffima an tada musu da kuruciya Allah ya kara basira breaker ya sa afi haka muna jiran ta gaba.

 

Waka Ce Mai Taba Zuciyar Masoya – Pretty Mardy

Gaskiya wakar ta yi dan tana taba zuciyar masoya, A nawa ganin babu wani burgewa ga yadda sirrin zaman auran ka a waje duk wani abu daya danganci soyayya a tsakanin ma’aurata yana bukatar sirri meye amfanin dorawa bideon kai da matarka kuna rawa wanda kasan dole akwai wanda kake kunya da zai gani tamkar ma baka kishin tane gaskiya wannan ba dai dai bane kuma babu wani birgewa a ciki kwata kwata.

 

In Da Ni Ce, Zan Yi Rawar Fiye Da Yadda Na Ga Suna Yi, Sai Dai… In Ji Deejat

A ra’ayina, wakar ta yi saboda baiti shine waka,ba sautin ba. Sannan rawar da aka yi gaskiya in nice zan yi fiye da hak ma mijina dan nuna soyayya amma gaskiya ba zan bari wata ta gan min miji ba dan ‘yan kwacen miji sun yi yawa a duniya.

 

Wakar Ta Yi Dadi Ba Kadan Ba – Ayshat Humaira

A gaskiya wakar ta yi dadi ba kadan ba, yayi kokari ya zuba kalamai na burgewa masu taba zuciya sai dai su matan da suka fito suka yi rawa da wakarsa kawai, kuma hakan ba lefin Hamisu bane, matan sune marasa hankali,shi tun yaushe yayi wakarsa? Ya ce musu su yi ne?, Naga mata da yawa sun yi hakan ra’ayi ne, domin dama akwai mata ai marasa tunani.

 

Wakar Ta Tsaru – Oum Khairat

Waka Kam ta yi kuma ta tsaru an yi amfani da kalamai masu dadi da tausasa rai , sai dai Kash rawar da aka watso a media ce ba ta yi ba.

 

 

Wakar Tana Mugun Kashe Min Jiki – Aglan Nissa

Kai Anty Rabi’a, wakar nan na mugun kashemin jiki walahi har kuka nayi farin jinta, sai na ji kamar…

soyaya rayuwa, wani sa’in sai tazom hutar kuna,

Duk wanda ke cikin shine jurau, amma fah a gurina,

So na faranta rai da ruhi yasa kazam kamar sarki,

kuma rayuwa da so misali zaina kama a mafalki,

Samari mu hakuri idan har mun samu so musa sauki,

‘Yan mata mu hakuri idan har mun samu so musa sauki, Masoyi yanada rana ne, masoyi yana da rana ne,

𝙂𝙖𝙨𝙠𝙞y𝙖 𝙬𝙖k𝙖𝙧 𝙣𝙖𝙣 𝙩𝙖 𝙮𝙞, 𝙧𝙖𝙬𝙖𝙧 𝙘𝙚 𝙠𝙖𝙬𝙖𝙞 𝙗𝙖 𝙩𝙖 𝙮𝙞 𝙗𝙖, Sako ya isa zuciyar masoya, gaskiya, amma an samu wasu magidantan mata sun yi amfani da ita wajan nuna nasu jahilcin, suna kunada ,suna rawa a gaban majajensu kuma suna watsawa a media dan tsabar rashin hankali, a gaskiya ni ko kawata mai aure , bana yarda taga mijina ba balle wasu jama’ar can daban.

 

Hatta ‘Yan Kudu Suna Son Wakar – Munneerah

Wallahi ta yi dadi ta kuma kankaro wa ‘yan arewa mutunci  har ‘yan kudu suna son wakar.  Wakar kam so mashaa Allah.  Amma batun manyan mata da suka yi rawa, Hamisu ba shi ya sa su ba,  Northern hibiscus ce, Kuma be dace ba suyi rawa su watsa a duniya ba.

 

Maza Da Matan Da Suka Taka Rawa Sun Birge Ni – Bintu

Ni kam wakar ta birge ni kuma mazan da matan ma sun birgeni wa ‘yanda sukata surutu kuma haushi ma suke ba ni. Abin da babu ruwanka me ya sa ka a ciki ni abin da ya sa ban yi ba ma saboda ba na ra’ayin Wa inda suka yi, wadanda suka yi kuma hakan ma ra’ayin sune so dan haka sun burgeni sosai da sosai.

 

Ni Kam Babu Birgewa A Ciki – Teemah Yusuf

Ni kam ba birgewa ba ne na fito da mijina a social Media ,hmm soyayya ya fi dadi daga ke sai mijinki wallahi ,ko naked (tsirara) ka yi rawa fine!

 

Masu Rawar Wakar Sun Karyata Masu Muzanta Mazanmu Na Arewa – Ummulkhairi

Game da gasar ‘dance for husband challenge’. Gaskiya ni kam sun burge ni, don yana nuna soyayya da shakuwa ne dake tsakanin miji da mata, sannan kuma yana karyata cewa da ake mazajen mu na arewacin Nijeriya basu san hakkin aure ba, maza na san mata kamar bayin su. Wannan yana karyata masu fadin haka.

 

 

Baitocin Wakar Kan Shigar Da Ni Shaukin Masoyina – Jannat

A gaskiya wakar JURUMAR MATA ta matukar dadi kuma na sara masa, domin  ya yi amfani da kalamai masu taushi da sanyi, wanda suke tsuma duk wata zuciyar da ta kasance ma’abociyar SO ce. ‘Especially’ ma baitukan nan nasa na farkon wakar inda yake cewa, “Ashe da rai nake son ki jaruma ba da zuciya ta ba, komai ruwa da iska a kan ki ba zana daina kewa ba, indai na samu zar samunki ba zana tanka kowa ba, ni banga mai harara ba bare na wai waya  ba.”

“Indai akanki ne zana jure wahalar tafiya garin nisa, da an tabaki a jirani danko tilas nazo na dau fansa, jimirin zuwanki nai dan kizo na kalleki gimbiyar hausa, sirri na rayuwata kece da kin kira dana amsa, zuma a biki dadi gareta kin bani taki na lasa, indai akan kine na yi nisan dan baki kiran da san amsa, tilasa ganin mu tilasa barin mu kaunarki tunda nai  nisa, sam ba batun na fasa ko da za’a ce in ba da rai fasa”.

Idan ina jin baitukan nan suna sani na shiga shauki da begen masoyina, zuciyata kuma tana kara tsuma da so da kaunar masoyina. Sai kuma wannan baitin nasa yakan sa na zubda hawaye inda yake cewa, “Ni ban da damuwa ina har zan bude dan idanuna, na kalleki gaki daf dani to mai za ya damu kalbina, yau zana yo amo tun da na gane kina da tausaina, dan yanzu na zamo ya  mafatauci mai bidar gurin kwana, na kwalla shela dan sanar da makiya malamai a, daga zuciya nake kwanta ina zayyano jawabaina, indan babu ke ina zan saka zuciyata tabar yawan kuna, kowa da nasa amma ni kece cikar muradaina.”

Hakika wannan baitin yana sani na zubda hawaye, saboda yana tuna min da yadda na yi nisa na abin so na. Sai kuma baitinsa inda yake cewa, “Yau gani a ruwa kusa da kada zo ki ceci karkona, komai da mafita karki saba da furta bankwana, ina ji ina gani yadda nake sanki yafi karfina, na san a duniya da wanda yake dauke duk tunanina, soyayya rayuwa wani saukin sai ta zama wutar kuna, duk wanda ke cikin shike jurau amma fa gurina.”

Da kuma inda yake cewa, “So na faranta rai da ruhi yasa saka ka zama kamar sarki, kuma rayuwa da so misaline na kama da a mafarki” Wannan bai tunkan ba karmin narkar min da zuciyata suke ba, suna sa ni na kara jin tsauyi masoyina da ma ni kaina gaba daya. Domin taushi kalaman cikin baitukan yayiwa zuciya yawa lokacin guda ta dauke su, amma kuma yayiwa zuciya kadan lokaci guda ta iya sarrafa su. Amma kuma  sun yiwa zuciya daidai wajen sanyayata, domin tsabar san yi dake cikin kalaman baitukan wakar gaba daya, yakan daskarar da duk wani abinda zai sha gabansu, zuciya ce kawai take da juriyar da za ta iya daukar wannan sanyi, har ta sarrafa su ba tare da wani shamaki ba.

Gaskiya na ji dadin wakar sosai, domin duk lokacin da nake cike da begen abin kaunata, idan na ji ta sai naji zuciyata ta fada cikin tafkin so da kauna da kuma nishadi da annashuwa. Gaskiya mawakin wakar ya yi kokari sosai, fatana gare shi, Allah kara basira da daukaka, hazaka, Allah ya daura sa a kan makiyansa, ya kuma kare sa daga sharin mutum ko aljan da karfe, dama sharin shi sharin da kansa. Ameen Ya Allah
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: