Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce da zarar ya zama shugaban kasa, kungiyar malaman Jami’a (ASUU) ba za ta sake fuskantar matsalar yajin aiki ba.
Atiku, ya bayyana hakan ne a wajen a bikin ranar matasa ta duniya a Abuja, a ranar Juma’a, inda ya ce mahaifinsa bai so ya je makaranta ba, amma daga baya ya jajirce har ya shiga makaranta har zuwa matakin jami’a.
Ya kara da cewa hakkin kowane matashi ne samun ilimi, inda ya ce yajin aiki da ASUU ke yi da kuma rashin magance matsalarsu da gwamnati ta gaza yi da cewa abin damuwa ne.
Ya kara da cewa hakan ba za ta taba faruwa ba a karkashin PDP ko kuma gwamnatinsa idan aka zabe shi.
Hakazaila, Atiku ya ce shi mutum ne mai bunkasa harkokin ilimi, inda ya kuma ce hakkin kowace gwamnati ne ta tabbatar an bai wa kowani matashi a kasar nan hakkokinsa musamman a bangaren ilimi.
ASUU dai na ci gaba da yin yajin aikin da ta tsunduma wajen watanni shi da.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp