Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce zai bude dukkanin iyakokin Nijeriya da ke rufe muddin aka zabe shi a 2023.
Atiku, ya bayyana hakan ne ga dubban magoya bayansa a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke Jihar Katsina.
- Kakakin Majalisar Dokokin Taraba Ya Yi Murabus, Kizito Ya Maye Gurbinsa
- Taliban Ta Haramtawa Mata Karatu A Jami’a A Afghansitan
A cewar tsohon Mataimakin Shugaban Kasar, “Yana daga cikin alkawuran da muka dauka na dawo da tsaro da tattalin arziki. Don haka zamu bude dukkanin iyakokin Najeriya da aka rufe.
“Idan kuka ba ni dama ba zan zama irin wanda zai sa a ci gaba harbin ’yan kasuwa saboda sun dauko buhun shinkafa ba,” cewar Atiku.
Dan takarar ya kuma ce dukkanin ababen more rayuwa da ci gaba da gwamnatin PDP ta baya ta gina a jihar, an salwantar da su.
Hakazalika, dan takarar ya ba da kyautar Naira miliyan 50 ga jama’ar da matsalar rashin tsaro ta shafa a jihar.
Ya bayar da kyautar kudin ne a fadar mai martaba Sarkin Katsina, Dokta Abdulmuminu Kabir Usman.
Atiku ya ce ya ziyarci Sarkin ne don neman tabarraki da shawara daga wajen shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp