Abba Ibrahim Wada" />

Zan Iya Barin Barcelona, In Ji Coutinho

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Philliph Coutinho, ya bayyana cewa bashi da tabbacin cigaba da zaman Barcelona bayan da rahotanni suka bayyana cewa kungiyar ta shirya sayar dashi a wannan kakar.

Coutinho ya koma Barcelona ne daga kungiyar kwallon kafa ta Liberpool a watan Janairun shekara ta 2018 sai dai tun daya koma kungiyar baya buga abinda akayi zaton zai buga wanda hakan ya sa a ka fara danganta shi da barin kungiyar.

A kakar wasan data gabata dai dan wasan ya buga wasanni 34 inda ya zura kwallaye biyar sannan kuma ya taimaka aka zura kwallaye uku sai dai wannan abinda yayi bai gamsar da kociyan kungiyar Barcelona da kuma shugabannin kungiyar.

Coutinho ya bayyana cewa sakamakon rashin jin dadin zaman Barcelona da kuma sukar da yake samu daga bangarori da dama ciki har da magoya bayan kungiyar ta Barcelona yasa yafara tunanin barin kungiyar domin neman inda zai dinga buga wasa yana jin dadi.

“Duk abinda kafafen yada labarai suke rubutawa ko kuma suke fada ba gaskiya bane sai dai tabbas akwai matsala a tattare da zamana a Barcelona amma kuma zan yanke hukunci idan an kammala kofin kudancin Amurka na Copa America” in ji Coutinho, wanda Barcelona ta biya fam miliyan 142 ta karboshi daga Liberpool

Dan wasan mai shekara 27 kungiyoyi da dama da suka hada da Chelsea da Paris Saint German da kuma Manchester United sannan itama tsohuwar kungiyarsa ta Liberpool tana neman sake sayansa

Exit mobile version