Zababben Shugaban karamar hukumar Garko a Jihar Kano Alhaji Salisu Musa Sarina yasha alwashin cewar zai yi iyakar mai yiwuwa a wajan kawo cigaba a karamar hukumarsa ta Garko da kewayanta a Jihar Kano gaba daya.
Shugaban karamar hukumar ta Garko Alhaji Salisu Musa Sarina ya yi wannan furuci ne jim kadan bayan dawowarsa gida Sarina daga duba wadansu ayyukan da ya gudanar a wadansu kauyuka da suka kunshi karamar hukumar sa ta Garko wadanda suka hada da magudanar ruwa da gyaran azuzuwan makarantun firamare da sakandire domin bunaasa harkokin ilimin karamar hukumar Garko da kewayanta a Jihar Kano da sauran makamantansu.
- IMMOWA Ta Horar Da Mata Da Yaran Jami’an Shige Da Fice Sana’o’i Â
- Da Dumi-Dumi: Sarauniyar Ingila, Elizabeth Ta Rasu
Ya cigaba da cewa adon haka nema ya ce nan bada dadewaba ma zai sake kirkiro makamantan irin wadannan ayyukan domin gabatar dasu asauran kauyukan da suka kunshi karamar hukumarsa ta Garko dake cikin birnin Kano gaba daya sannan ya shawarci matasansa na karamar hukumar dama Jihar Kano baki daya da su rungumi akidar neman ilimin zamani dama na arabiya domin samun ingantaccan ilimin da zai kara inganta harkokin rayuwarsu ta duniya dama lahira baki daya.
Ya kuma shawarci matasan na Jihar Kano da sauran al’umma da su kara kokari a wajen rungumar akidar neman zaman lafiya tare da neman na kansu domin su samu tsayawa da kafafuwansu a wajen kaucewa shiga halin kakanikayi da sauran al’amuran da suka shafi harkokin rayuwar su ta yau da kullum gaba daya, sannan kuma ya jinjina wa Gwamnatin Jihar Kano a karkashin jagorancin Gwamnan Jihar ta Kano Dakta Alhaji Abdullahi Umar Ganduje a kokarinsa na kawo kyawawan ayyukan da suke cigaba da ciyar da jihar ta Kano gaba dama harkokin rayuwar al ummar jihar ta Kano gaba daya a karshe ya ce yanayi wa al’ummarsa ta karamar hukumar Garko da Jihar Kano dama Nijeriya baki daya fatan alheri na cigaba da kara samun zaman lafiya.