Sulaiman Bala Idris" />

Babbar Magana… Zan Yi Takara A Shekarar 2019 –Buhari

Wannan Damuwar APC Ce –PDP

Bai Kamata A Sake Zabensa Ba –Farfesa Moghalu

A jiya ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana aniyarsa wacce aka jima ana sauraron jin ta, na sake tsaya wa takarar shugabancin Nijeriya a shekarar 2019.

Shugaban Kasar ya ayyana wannan aniya ta sa ne a wurin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC wanda ya gudana a Babban Birnin Tarayya, Abuja.

A wata takarda da ofishinsa ya fitar, ya tabbatar da batun sake tsayawa takarar Shugaban Kasan a kakar zaben 2019 mai zuwa.

Ofishin ya ce, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ayyana aniyarsa ne a wani taron sirri da ya yi da masu ruwa da tsakin jam’iyyar APC.

Shugaban Kasan ya ce, wannan ayyanawa ya biyo bayan irin matsin lambar da ya samu daga ‘yan Nijeriya na son ya sake tsayawa takara a shekarar 2019. Ya kuma ce, ya sanar da shirin takarar ne a gaban masu ruwa da tsakin jam’iyyar don ya zama su ne na farko da suka san da shirin nasa.

Kafin ya ayyana batun takarar tasa, sai da shugaban kasan ya gabatar da jawabi dangane da rahoton da kwamitin bibiyar lamurra ya gabatar ga masu ruwa da tsakin jam’iyyar.

Sai dai a nata martanin, Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa, ayyana sake tsayawa takarar Shugaba Buhari ba damuwar al’ummar Nijeriya ba ce, damuwa ce ta cikin gidan jam’iyyar APC.

Wannan martani na PDP ya fito ne daga bakin mai magana da yawun jam’iyyar, Kola Ologbondiyan. Inda ya ce, wannan ayyanawa ba ta zo musu da ba-zata ba, kuma ta jefa Buhari ne a cikin jerin masu fafutukar neman kujerar Shugabancin Kasa a shekarar 2019. “Ba za mu bata lokacinmu akan wannan ayyanawa ba, har sai ranar da APC ta ba shi tutar takarar 2019”.

Shi ma a na shi bayanan, dan takarar Shugaban Kasa, Farfesa Kingsley Moghalu ya bayyana cewa, Buhari na da ikon ya ayyana yin takara. “Sai dai, kamar sauran miliyoyin ‘yan kasa, bana tunanin Buhari ya cancanci a sake zabensa sakamakon irin gazawar da ya nuna wurin ciyar da kasar nan gaba.

“Yan Nijeriya na bukatar  wani sabon salon shugabanci wanda zai hada kan ‘yan kasa, ya kawar da kangin talaucin da ya yiwa al’ummarmu katutu – ta yadda a yanzu Nijeriya ta koma tamkar Babbar Birnin Talauci ta duniya, wacce ke da kaso mafi tsoka na talakawa. Inda ake da irin wannan bai kamata ma Shugaban ya sake neman a zabe shi ba”. inji Farfesan

 

Exit mobile version