Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, ya ayyana dokar hana fita ta awa 24 sakamakon satar dukiya da lalata abubuwa yayin zanga-zangar matsin rayuwa ta #EndBadGovernance.
A wata sanarwa da ya yi wa jihar a daren Alhamis, Gwamna Namadi ya nuna damuwarsa kan lalata dukiyoyin, yana mai cewa irin wannan hali ba ya nuna al’adu da halin ƴan jihar.
- Jihar Zamfara Ta Lashe Gasar AlKur’ani Ta Ƙasa Ta Mata
- Ɓata-gari Sun Cinna Wa Sakatariyar APC Wuta Tare Da Lalata Kadarorin Gwamnati A Jigawa
Ya jaddada cewa yayin zanga-zangar an yi amfani da ƙananan yara don lalata dukiyoyin jama’a, wanda ya sanya tilas a sanya dokar hana fita. Dokar hana fita za a sassauta daga karfe 12:00 na rana zuwa 2:30 na yamma ranar Jumma’a don bai wa jama’a damar yin sallar Jumu’ah.
Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Jigawa ta sha alwashin tabbatar da bin dokar hana fita sosai. DSP Lawan Shiisu Adam, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ya ba da rahoton cewa tarzomar yayin zanga-zangar ta haɗa da hare-hare kan shaguna, da sakatariyar ƙananan hukumomi, da gidajen ‘yan siyasa.
Kawo yanzu dai an kama mutune hamsin da biyar, kuma an samu kaya daban-daban da suka haɗa da babura, da kekuna, da buhunan takin zamani, da kujeru, da kuma akwatunan gidan sauro.
Masu zanga-zangar sun kuma ƙona motoci shida a Sakatariyar ƙaramar hukumar Hadejia, da sun lalatawa gami da kwashe kayan a shagon JARDA a Gumel, sun kuma ƙona gidan ɗan majalisar, da sun lalata ofishin NITDA, da kwashe kaya kuma sun ƙona ofishin jam’iyyar APC na jihar, sannan sun yi yunƙurin kai hari gidan Sanata Babangida Hussaini a ƙaramar hukumar Kazaure.
Dokar hana fitar za ta ci gaba har sai an sake nazarin yanayin kuma an yanke shawara ta gaba.