Tsohon Hafsan Sojin Kasan Nijeriya Laftanar-Janar Tukur Yusuf Buratai, ya yi barazanar maka kafar yada labarai ta yanar gizo wato Sahara Reporters a kotu.
Buratai wanda a yanzu Jakadan Nijeriya ne a Jamhuriyar Benin ya kuduri daukar matakin ne saboda danganta shi da kafar ta yi kan zargin badakalar Naira biliyan 1.85 da EFCC da ICPC suka bankado a wani gidansa da ke a birnin tarayyar Abuja wanda kuma kafar ta wallafa.
- Gwamnati Ta Kusa Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU – Sabon Minista
- Dakarun Sojojin Nijeriya Ku Ci Gaba Da Kasance Wa Cikin Shirin A Koyaushe —COAS
Tuni dai, Buratai ya danganta rahoton a matsayin na karya kuma wanda bai da wani tushe ballanta makama.
A ranar 8 ga watan Julin 2022 ne Buratai ta hanyar lauyansa Reuben Atabo (SAN), ya danganta rahoton a matsayin maras tushe ballanta makama, inda kuma ya bukaci kafar da ta gaggauta janye rahoton tare da kuma neman yafiyarsa.
Buratai ya kuma yi nuni da cewa, labaran na karya da kafar ta wallafa zai iya sanya wa al’umma su ki jininsa da kuma janyo a afka masa, inda ya kara da cewa, rahoton na kaharu wanda kafar ta wallafa zai ya bata masa suna da kimarsa da kuma mutuncinsa, mussaman a matsayinsa na Jakadan Nijeriya a Jamhuriyar Benin.