Khalid Idris Doya" />

Zargin Dogara A Kan Gwamnan Bauchi Kan Kwangiloli Ba Shi Da Tushe – Adamu Khadah

gwamnan Bauchi

Wani dan kwangila a jihar Bauchi mai suna Adamu Alhaji Ahmad ya musanta zancen da tsohon shugaban Majalisar wakilai Hon. Yakubu Dogara ya taba yi da ke zargin gwamnan jihar Bauchi da nuna ‘yan uwanci da bangaranci a yayin rabon kwangilolin da ake yi a jihar.

A cewarshi shi shaida ne kuma daya daga cikin wadanda suka amfana da kwangilar gwamnan, duk da ya ce babu wata alaka ko ta kusa ko ta nesa da ta hada shi da gwamnan illa iyaka shi dan asalin jihar ne mai cikakken damar neman kwangila kamar kowani mai kamfani.
Idan za ku iya tunawa dai bayan da Yakubu Dogara ya fice daga jam’iyyar PDP, ya yi wasu maganganun da suke bayyana irin barranta da ya yi da tafiyar Gwamna Bala inda ma ya zargi gwamantinsa da kasa-kasau tare da yin zargin cewa gwamnan na baiwa ‘yan uwansa da abokansa fifiko wajen rabon kwangiloli a jihar.
A martanin na Adamu Ahmad yayin wani taron manema labarai da ya kira, ya nuna cewa gwamnan jihar na Bauchi na bayar da kwangiloli bisa cancanta da dacewa tare da bin dukkanin matakan da suka dace wajen rabon kwangiloli ga wadanda suka nema.
Adamu wanda shine Manajan Darakta na kamfanin ‘KHADAH Imperial Synergy Limited’ ya yi tutiyar cewa kamfanin nasa bai da wata alaka ko ta abota da gwamnan amma ya amince da baiwa kamfanin nasa kwangilar gina wasu asibitoci a jihar bayan da suka ce bukatar nema.
“Batun wai gwamnan Bauchi na rabar da kwangiloli ga abokansa da ‘yan uwansa babu gaskiya a wannan batun, sam ba haka zancen ya ke ba, ina mai karyata wannan batun. Gwamnan Bauchi ya baiwa kamfaninmu aikin kwangila, a lokacin bai ma wuce wata uku zuwa hudu a matsayin gwamna ba. Ya ba mu aikin ne kawai a sakamakon gamsu da takardunmu da muka tura na neman aikin bayan mun bi duk matakai na nema. A kan haka ne aka ba mu kwangila muka fara aiki.
“Asibitin da aka ba mu aikinsa babban asibiti ne mai dauke da abubuwan nema. Bisa cancantarmu ne aka ba mu ba tare da shi gwamna ya sanni ba. Yanzu haka idan muka yi ido biyu da gwamna ba zai iya kiran sunana ba don bai sanni ba, amma mun nemi kwangila bisa dacewa da yadda doka ta tanadar an ba mu bisa hakan.
Don haka da ya ce maganar da Hon. Dogara ya yi ta cewa gwamnan na rabon kwangila ga abokai da ‘yan uwa zargi ne mara tushe balle makama.
Adamu ya kuma shaida cewar baya ga shi, akwai wasu ‘yan kwangiloli da daman gaske da suka samu aiki a karkashin gwamnan jihar ba tare da ma gwamnan ya san su ba, “Illa kawai ya ba su kwangila bisa cancanta da dacewar kamfanoninsu.
Daga bisani ya roki gwamnan jihar da cewa ya taimaka ya daina biye wa ‘yan siyasan da ke neman karkatar da hankulansa daga aiyukan da ke gudanarwa.

Exit mobile version