Wasu fusatattun matasa a daren ranar Asabar sun kona wata keken ‘Adaidaita Sahu’ kan zargin masu keken da hada baki wajen kwacen wayoyin salular mutane.
Lamarin ya faru ne a kan titin Ibrahim Taiwo da ke cikin birnin Kano.
- Kotun Daukaka Kara Ta Ayyana Ranar Yanke Hukunci Kan Neman Tsige Sarkin Zazzau
- Yadda Matasa Masu Kananan Shekaru Ke Zuwa Neman Aurena Na Matukar Daure Min Kai -Hadizan Saima
Fusatattun matasan sun kama wadanda ake zargin sannan suka mika su ga jami’an tsaro bayan sun kona kekensu.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yansandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa wadanda ake zargin suna hannun ‘yansanda.
Kiyawa ya kara da cewa, an kwato wayoyin hannu guda biyar daga hannun wadanda ake zargin.