An gudanar da babban taron shugabannin majalisun kasa da kasa karo na 6 daga ranar 29 zuwa ta 31 ga watan Yulin bana a birnin Geneva, inda shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Zhao Leji ya halarci zaman tare da gabatar da jawabi mai taken “Rungumar manufar cudanyar sassa daban daban, a kokarin kafa duniya mai kyau”.
A cikin jawabinsa, Zhao ya bayyana cewa, yanzu haka ana fuskantar munanan kalubaloli a fannin wanzar da zaman lafiya, da ci gaban dan Adam. An kuma dora wa majalisun kafa dokokin kasa da kasa alhakin kara azamar kafa sabuwar hulda tsakanin kasa da kasa. Ya ce, wajibi ne a kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, a kara azama kan samun ci gaba da wadata a duniya, a kuma sa kaimi kan yin mu’amala, da koyi da juna ta fuskar wayewar kai, a kuma kara azama kan samun adalci a duniya.
Zhao ya jaddada cewa, majalisar wakilan jama’ar kasar Sin na son inganta mu’amala, da hadin kai da kawancen majalisun kasa da kasa, da majalisun kafa dokokin kasa da kasa, wajen aiwatar da shawarar ci gaban duniya, da shawarar tsaron duniya, da shawarar wayewar kan duniya tare, a kokarin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan dan Adam cikin hadin gwiwa.
A wata sabuwa kuma, Zhao Leji ya gudanar da ziyarar sada zumunta a kasar Switzerland, daga ranar 28 zuwa ta 31 ga watan Yuli, bisa gayyatar da shugabar majalisar wakilan Switzerland Maja Riniker, and shugaban majalisar dattawan Switzerland Andrea Caroni suka yi masa. (Tasallah Yuan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp