An so idan akwai hali, mai ziyara ya yi kwana takwas a Madina yana gabatar da sallolin farillan nan guda biyar
tare da Annabi (SAW) a Masallacinsa. Ma’ana mutum yana sallah ga kuma Annabi (SAW) a Masallacin.
Idan kuma Hukumar Alhazai ba ta bari ba, shikenan. Ko na kwana daya mutum ya yi da Annabi (SAW) ya isa dukkan falala.
Dole ne ko wane Musulmin Kwarai ya girmama Manzon Allah (SAW) ya daraja shi tare da bin sa.
A cikin Alkur’ani maigirma Allah (SWT) ya ce, &kuot;Mu muka aiko ka – ya Rasulallahi a matsayin – maishaida, maibishara, maigargadi (ga al’ummarka), – ku kuma al’ummarsa – ku yi imani da Allah, da Manzonsa, ku daraja shi, ku kai matukar girma wurin daraja shi.&kuot;
Malam Mubarridu ya ce ma’anar &kuot;wa tu’azziruhu&kuot; a cikin ayar ita ce &kuot;ku kai matuka cikin girmama Manzon Allah (SAW).
Don haka Musulmi kar su yarda wani ya rude su ya yi musu dodorido idan an ga suna girmama Annabi (SAW) a ce musu ‘yan bid’ah sai su ji shakka su daina. Da irin wannan fahimtar ce aka je aka tada wa Annabi (SAW) bom a Masallacinsa.
Hatta Sahabban Annabi (SAW) sun fuskanci irin haka, babu abin da ba a fada musu ba, an ce musu wawaye saboda sun yi imani kuma duk abin da Manzon Allah (SAW) ya ce su yi ba sai sun tambaya ba, kawai yi suke.
Malamai sun bayyana cewa girmama Manzon Allah (SAW) bayan rasuwarsa, daidai yake da girmama shi kamar lokacin da yake da rai, babu banbanci. Kamar yadda ka san idan ka je gabansa yana raye za ka yi ladabi, haka ma yanzu idan ka je kabarinsa.
Yana daga girmama Manzon Allah (SAW) idan za ka ambaci sunansa, kar ka yi kamar na sauran mutane, ka sanya ladabi da natsuwa. Shi ya sa galibi masoyansa suka fi kiran mutanen da aka sanya musu sunansa (SAW) da lakabi. Maimakon Muhammadu, sai a rika fadar lakabin Nura, Hadi, Amin, Kamal, Nazir, Kamil da sauran su. Sannan da an ambaci sunan ka yi ma sa salati.
Haka nan yana daga girmama shi (SAW), idan mutum zai karanta Hadisinsa, ya yi shiga mai kyau tare da natsuwa da kankantar da kai. Haka nan ya girmama Sunnarsa.
Ma’anar Sunnah ita ce abin da Annabi (SAW) ya yi ko ya umurci a yi ko kuma aka yi a gabansa bai hana ba.
Amma ba kamar yadda wasu ke dauka ba musamman a kwanan nan, raina Allah da Manzonsa da wulakanta darajojin iyalan gidan Annabi (SAW) da sahabbansa a matsayin Sunnah.
Yana daga girmama Manzon Allah (SAW) da son sa, mutum ya rika shaukin jin tarihinsa da girmama iyalan gidansa da sahabbansa da malaman Musulunci magada Annabawa da duk wani abu da ya rataya da shi (SAW). Tun daga kan garin da ya zauna a ciki, da gidansa, da kayan da ya yi amfani da su har ma da ire-iren abincin da ya fi so da suturar sawa, duk a so su, a ga girmansu, ballantana kuma kabarinsa
Ya zo cikin Hadisi madaukaki cewa &kuot;Mumini ana binne shi ne a kasar da aka gina shi da ita.&kuot; Ma’ana duk inda aka binne mutum, da kasar wurin ne aka kwaba aka yi halittarsa da ita.
Kenan kasar Madina tana da matukar girma, don da ita ce aka gina Manzon Allah (SAW) da ita. Koda yake za a iya cewa ta yaya aka haife shi a Makka ba a Madina ba? To Abdullahi bin Abbas (RA) ya ruwaito Hadisin da cewa &kuot;lokacin da aka yi ruwan dufana ne Allah ya tafiyar da kasar halittarsa (SAW) zuwa Makka.&kuot;
Saboda haka kamar yadda Annabi (SAW) ya kasance mafificin Dan Adam, to kasar da aka yi halittarsa da ita ita ce mafificiyar kasa. Kuma shi ya sa Manzon Allah (SAW) ya ce &kuot;Ba domin yin Hijira – don Zatin Allah – ba (daga Makka zuwa Madina) da a Madina ma aka haife ni&kuot;. Tirmizi ya ruwaito Hadisin.
Domin fitar da abin a fili ma, Kakar-Kakar Manzon Allah (SAW) Salma’a wadda ta auri Hashimu ‘yar Madina ce daga kabilar Banin Najjar. Haka nan don Allah ya nuna wa mutane lamarin, sai Mahaifinsa Sayyidina Abdullahi (RA) ya zo ya rasu a Madina a lokacin da ya ziyarci dangin Kakarsa Salma’a. A da akwai gidan da ake zuwa ana ziyarar kabarin Kafin Ahlu Sa’ud su kama Madina su rufe wurin.
Ita ma Mahaifiyarsa Sayyida Amina (RA) ta ziyarci mijinta, Baban Annabi (SAW) tare da shi, da Ummu Aimana, a kan hanyarta ta komawa daga Madina ta rasu a Ab’wa. Daga Madina zuwa Ab’wa kilomita 150 ne. Amma tsakanin wurin da Makka kilomita 250.
Ibn Baddalu ya ce &kuot;Kamshin Madina ya ninka na ko ina&kuot;. Imamu Malik (RA) ya yi fatawa a yi wa wani mutum da ya ce kasar Madina lalatacciya ce bulala 30 kuma a kulle shi a kurkuku. Sai aka ce ma sa wannan mutumin babba ne fa? Sai ya ce &kuot;Ai ba bulala ya dace a yi ma sa ba, a daki wuyarsa kawai.&kuot; Ma’ana a kashe shi.
Akwai sabani a kan wadda ta fi daraja tsakanin Makka da aka haife shi (SAW) da Madina wadda ya yi Hijira kuma ya rasu a can. Ko wacce akwai Sahabbai da Malamai da suka goyi bayan fifikonta. Amma a wurin mu Malikawa, Madina ta fi daraja.
Sannan da Malikawan da sauran malaman Maz’habobin duk sun yi ittifakin cewa nan Shabbakin Manzon Allah (SAW) da ke kunshe da jikinsa ya fi ko wane wuri a kan kasa. An ciro wannan ne daga Tajuddinis subki. Shi kuma ya sake cirowa daga Ibn Akilul Hambali cewa &kuot;Wurin da aka binne Manzon Allah (SAW) ya fi har Al’arshi&kuot;.
Za mu dakata a nan sai Allah ya kai mu mako mai zuwa insha Allahu. Wa sallallahu alal fatihil khatimil hadiy wa ala alihi hakka kadirihi wa mikdarihil aziym.