Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya yi bayani game da ziyarar da shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki zai kawo kasar Sin, inda yake imanin cewa, ziyarar za ta sanya sabon kuzari a dangantakar Sin da Eritrea a dukkan fannoni da ma ci gaba da raya dangantakarsu ta abota.
Bisa gayyatarsa da shugaba Xi Jinping ya yi, shugaba Isaias Afwerki zai fara ziyarar aiki a kasar Sin daga ranar 14 ga wata. (Fa’iza)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp