Yayin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ke gudanar da ziyarar aiki yanzu haka a kasar Sin, masharhanta da dama na ganin wannan ziyara wadda ita ce irinta ta hudu da yake gudanarwa a Sin, ta wuce batun raya huldar diflomasiyya kadai, domin kuwa ziyarar za ta samar da wani zarafi mai kima, da damammaki masu tasirin gaske ga Turai, a fannin bunkasa kirkire-kirkire da jagorancin duniya. Yayin da ake ganin sauye-sauyen al’amuran duniya cikin sauri, bai kamata sashen Turai ya bari a bar shi a baya ba.
Tuni dai kasar Sin ta zamo babbar cibiyar tattalin arziki da fasahohin zamani a duniya. Ga kasashen Turai, ciki har da Faransa, lokaci ya yi da za su gaggauta hade kamfanoninsu da sassan da su ne makomar gobe a fannin raya tattalin arziki. Misalin wadannan sassa sun hada da na raya ababen hawa masu tashi kusa da doron duniya, da masu amfani da makamashi mai tsafta, da fannin raya birane, da kere-keren mutum-mutumin inji zuwa fasahar kirkirarriyar basira ta AI.
Shugaba Macron na da damar ingiza karsashin Turai, da tabbatar da nahiyar ta zamo abokiyar tafiya, ba wai kawai kasuwa shigar da hajoji ba. Tafiyar hawainiya a wannan fanni na iya haifarwa Turai matukar koma baya, musamman a gabar nan da Sin, tare da sauran kasashe masu samun saurin bunkasa ke da tasirin kara mamaye makomar duniya a gwamman shekaru masu zuwa.
A ganina wannan ziyara da shugaban Faransa ke yi yanzu haka a kasar Sin, kamata ya yi ta zamo damar kara azamar tsara matakan hadin gwiwa da Sin, ta yadda Faransa za ta ingiza tsarin raya nahiyar Turai daga fannoni daban daban. Domin kuwa, a yayin da duniya ke samun saurin sauyin fasahohin zamani, babu zabin yin jinkiri, wajibi ne a gaggauta shiga tafiyar neman ci gaba tare.
Tabbas hadakar tafiya tsakanin Sin da Turai ta shallake batun samun moriyar tattalin arziki kadai. Ya kamata ziyarar shugaba Macron ta wannan karo ta gaggauta sauya tsarin jagorancin mabambantan sassan duniya ta yadda Sin da Turai za su samu karin zarafi na raya kansu tare.
Ko shakka babu, wannan ziyara ta shugaba Macron dama ce da ba kasafai a kan same ta ba, don haka ya wajaba a yi himmar cin gajiyarta. Lokaci ne da ya kamata Faransa da Turai su shigar da kansu muhimmin dandalin kirkire-kirkire da jagorancin duniya, domin kaucewa zama ’yan kallo a nan gaba. (Saminu Alhassan)














